’Yan asalin garin Chibok sun kai wa Gwamna Fashola kukansu

’Yan asalin garin Chibok da ke zaune a Jihar Legas sun yi kira ga Gwamna Babatunde Raji Fashola ya taimaka wajen ganin an sako sauran ’yan matan da ’yan kungiyar  boko haram suka sace a garin na Chibok da ke Jihar Borno.dalibai kimanin maitan da talatin (230) ake zargin ’yan kungiyar boko haram sun sace […]

’Yan asalin garin Chibok sun kai wa Gwamna Fashola kukansu
’Yan asalin garin Chibok sun kai wa Gwamna Fashola kukansu

’Yan asalin garin Chibok da ke zaune a Jihar Legas sun yi kira ga Gwamna Babatunde Raji Fashola ya taimaka wajen ganin an sako sauran ’yan matan da ’yan kungiyar  boko haram suka sace a garin na Chibok da ke Jihar Borno.
dalibai kimanin maitan da talatin (230) ake zargin ’yan kungiyar boko haram sun sace daga makarantarsu da ke Chibok din fiye da makonni biyu da suka gabata, amma har hada wannan rahoton, akwai kimanin dalibai 187 wadanda ba a gano inda suke ba ma, balle a sako su.
’Yan asalin garin Chibok sun yi kiran ne lokacin da suka yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar da ke yankin Ikeja.
Mutanen, wadanda sun kai su kimanin 50 maza da mata, sun nemi Gwamna Fashola ya matsa wa gwamnatin tarayya da duk wadanda suke da ruwa da tsaki wajen kubutar da ’yan matan lamba don a sako su.
Shugaban tawagar kungiyar, Mista Moses Zakwa ya ce al’amarin ya tayar musu da hankali. “Hankalinmu ya tashi a lokacin da muka samu labarin aukuwar lamarin. Mun damu kwarai da gaske, kuma muna bukatar taimako. Gwamna Fashola, mun san wannan abu ya auku a wajen Legas, amma muna rokon ka yi duk abin da za ka iya don ganin an kubutar da yaranmu”. Inji shi.
Shi kuma Gwamna Fashola ya yaba wa kungiyar da yadda suka bi hanyar da ta dace wajen gabatar masa da bukatunsu.
Ya bayyana garkuwa da mutane a matsayin babban laifi da mai tsoro ne ke aikata shi. Sannan ya bukaci kada su dauka ba a yin komai dangane da kubutar da yaran, amma sai ya ba su tabbacin cewa hukumomin da lamarin ya shafa suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kubutar da yaran.