’Yan Awawa sun wawashe dukiyar mutanen Agege
Wata sabuwar kungiyar zauna-gari-banza da suka yi wa kansu lakabi da ‘Awawa Boys’ sun addabi mutanen Agege da fashi da makami tare da yi wa duk wanda suka gamu da shi kwace. ‘Awawa’ kalma ce ta Yarabanci wacce da Hausa take nufin ‘A zo a same mu’ ko ‘A zo muna nan’Binciken Aminiya ya gano […]
Wata sabuwar kungiyar zauna-gari-banza da suka yi wa kansu lakabi da ‘Awawa Boys’ sun addabi mutanen Agege da fashi da makami tare da yi wa duk wanda suka gamu da shi kwace.
‘Awawa’ kalma ce ta Yarabanci wacce da Hausa take nufin ‘A zo a same mu’ ko ‘A zo muna nan’
Binciken Aminiya ya gano cewa yaran, wadanda shekarunsu na haihuwa ya kama daga 18 zuwa 25 suna tafiya ne gungu-gungu, mata da maza dauke da makamai suna yi wa mutanen da ke zaune a unguwannin Agege fashi tare da yi wa mata fyade.
Bello Aminuda ke zaune a Layin Adeniyi, yana daya daga cikin wadanda ’yan Awawan suka shiga gidansa. Ya bayyanna wa Aminiya cewa yaran sun shiga gidansa da misalin karfe biyu na dare.
“Da misalin karfe biyu na dare ina barci sai na ji makwabcina yana ihu barawo-barawo. Ban Ankara ba sai kawai na ji sun fara karya kofar gidana. Da na lura za su balla kofar da karfi sai na ce su tsaya zan bude musu. Ina bude kofar sai kawai suka shigo suna tambayata kudi. Nan take suka dauke mini fiye da dubu casa’in da wayoyina na hannu guda hudu da talabijin dina ta bango da sauran abubuwan kudi masu yawa. Nan take suka rika dukana bayan na ba su kudin sai suka buga mini wani abu a kai. Nan take jini ya rika zuba. Kamar zan mutu a cikin dare. Daga bisani ’yan sanda suka zo suka kai ni asibiti aka yi mini dinki aka sanya mini magani.” Inji shi.
Wani dattijo dan shekaru 70 da haihuwa da ke zaune a Layin Kwakwa-Uku mai suna Jakob Adetola, ya bayyana cewa sun shiga gidansa da misalin karfe uku na yamma.
“Suna zuwa sai kawai suka karya taga da kofar gidana, suka shigo. Sun dauke mani kimanin Naira dubu 17 suka rika dukana da matata da ’ya’yana. Na gan su sun kai su kimanin 20 shekarunsu sun kama daga 18 zuwa 20. Ban kai kara wurin ’yan sanda ba saboda ba abin da za su yi sai dai su ci mini kudi.” Inji shi.
Shi ma Abudurrafi’u Eto da ke Layin Kwakwa-Uku mai sana’ar dinkin ya bayyana cewa sun shiga shagonsa da karfi sun yi masa fashi.
Ya ce: “Ina cikin dinki da tsakar dare sai na ji wucewarsu, har sun wuce amma sai na ji sun yi harbi da bindiga, sai na ji suna cewa mu shiga gidan nan. Suna zuwa sai suka karya kofar gidanmu, suna shiga sai suka yi kokarin karya kofata, sai na rike kofar shagona na hana su shiga. Daga bisani sai suka sanya diga suka karya kofar da karfi, bBa su sami kudi a wurina ba sai dai wayata amma duk ’yan gidanmu sun kwace musu kudi. Ni kuma suka dake ni saboda ba su sami kudi a wurina ba.
Magajin Garin Agege, Alhaji Ali Abubakar Zango, ya bayyana cewa masarautar Agege ta dauki matakan da suka dace wajen ganin an yi maganin ’Yan Awawa.
“Ba mu bata lokaci ba, nan da nan muka kira taro muka rubuta takarda zuwa ga Kwamishinan ’yan sanda da Shugaban hukumar SSS na kwamandan sojoji na Legas, muka yi korafi kan abubuwa da suka faru. Kuma da taimakon Allah har an kama wasu daga cikin wadannan yara, dukkansu sun gudu kuma jami’an tsaro sun tashi tsaye don ganin sun kamo sauran. Lamarin ya nemi ya ta’azzara don a rana daya sai da yaran suka shiga gidaje 25 kuma akwai lokacin da suka yi fashi a lokaci daya a rana daya a sassa daban-daban na Agege. Saboda haka muna yin duk abin da za mu yi don ganin cewa an kawo karshen ’yan Awawa da wasu bata gari a Agege.” Inji magajin garin.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Kenneth Nwosu ya ci tura domin a lokacin da Aminiya ta kira shi ta wayar salula sai ya ce yana tuki a tura masa sakon waya amma har zuwa lokacin kammala rubuta wannan rahoto bai kira wakilinmu ba kuma bai bayar da amsar sakon wayar da wakilinmu ya tura masa ba.