‘’Yan babura na kashe mana yara ta hanyar tukin ganganci a Gombe’
Yara ne kanana suke hawa babura sababbi kirar UD suna gasar tsere a cikin gari a lokacin daukar amarya ko kuma sai sun ga babbar mota za ta wuce, sai ka ji sun ce ‘sa ta kawai’
Mazauna garin Gombe na kokawa kan yadda matasa masu hawa babura kirar UD suke haifar da hadurra a garin, inda kusan kullum sai sun karya yara, musamman a ranakun Juma’a da Asabar da ake bukukuwan daurin aure.
Wani magidanci mai suna Yusuf Muhammad da ke zaune a unguwar Jekadafari a garin Gombe, ya ce yanzu haka dansa na kwance a gida dan UD ya kade shi saboda irin gudun ganganci da suke yi a gari, kuma babu wanda yake a iya yi wa su wadannan masu baburan magana.
Ya ce, “Yara ne kanana suke hawa babura sababbi kirar UD suna gasar tsere a cikin gari a lokacin daukar amarya, ko kuma sai sun ga babbar mota za ta wuce, sai ka ji sun ce ‘sa ta kawai’, su shiga ta karkashinta.”
Magidancin ya koka kan rashin tsawatar wa yaran ko dokar da za a kama su su rika fuskantar hukunci da hakan zai rage wannan rashin hankali da suke yi.
Sai ya yi kira ga gwamnati ta kafa wata doka da za ta sa a kama a kuma hukunta masu irin wannan dabi’a domin a samu sauki a garin; Saboda rashin dokar ce ta sa masu babur mai kafa uku da yara ’yan UD suke takarya mutane.
A bangarenta, Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) Reshen Jihar Gombe, Kwamandan hukumar, Isiyaku Gammi Ibrahim, ya ce saboda yadda aukuwar hatsari ya yawaita, daga watan Disamba zuwa watan Janairun da muke ciki, sun samu rahoton aukuwar hatsari 50 kuma mafi yawa daga ciki na ’yan babura ne.
Ibrahim ya ce hakan ce ta sa suka baza jami’ansu a kan hanyoyi don kare aukuwar hatsari da kuma rage cunkoson ababen hawa.
Ya bayyaan cewa idan hukumarsu ta kama yara kanana suna tuka babura masu kafa uku ko baburan UD, kwacewa hukumar take yi, sannan su kira iyayen yaran domin su yi belin su su kuma yi musu gargadi.