’Yan bandiga sun kashe hakimi a Taraba

’Yan bandiga sun halaka hakimi a Taraba

’Yan bandiga sun kashe hakimi a Taraba

‘Yan bindiga

Wasu ’yan bindiga sun halaka hakimin garin Sarkin Kudu da ke Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Wata majiya a yankin ta shaida wa wakilin Aminiya cewa ’yan bindigan sun afka fadar hakimin mai suna Ali Hakimi da misalin karfe 12.30 na daren jiya.

Majiyar ta ce ’yan bindigan sun tilasta wa hikimin fitowa daga dakinsa zuwa kofar fadarsa ta hanyar nuna masa bakin bindiga.

A kofar fadar hakimin ne ’yan bindigan suka harbe shi har lahira sannan suka tsere, har yanzu ba a gano su ba.

Ali hakimi kani ne ga sarkin masarautar Sarkin Kudu, daya daga cikin masarautun da tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya kirkiro a lokacin mulkinsa.

Kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya ci tura, domin wayarsa a kashe a lokacin da wakilin, mu ya kirashi dangane da labarin.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta