’Yan banga ba su da hurumin ɗaukar doka a hannu — Kwamishinan ’yan sanda
Kwamishinan ya ce dole ne su tsaftace aikinsu don gudun ɗaukar doka da hannunsu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Hayatu Usman, ya gargadi ’yan banga da su guji ɗaukar doka a hannu a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a jihar.
Kwamishinan, ya yi gargadi ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ofishin ’yan sanda da ke Kananan Hukumomin Nafada da Bajoga a jihar.
- Alkawuran NLC ba za su cika a lokaci guda ba — Gwamnatin Tarayya
- Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 4, sun ceto mutum 11 a Kaduna
Ya ce, ’yan banga jami’an sa-kai ne da ke sadaukar da rayuwarsu wajen tsaron al’ummarsu, don haka ya gargade su da su guji cin zarafin al’umma ta hanyar daukar doka a hannunsu.
“Ina alfahari da ku sannan ku sani ku abokan aikinmu ne da suke taimakawa wajen samun nasara wajen dakile laifuka,” in ji Kwamishinan.
Ya kara da cewa ‘yan bangar na bayar da gudunmawa mai tarin yawa, musamman wajen kai samame dazuka don fatattakar masu aikata laifuka a jihar.
Sai dai Kwamishinan ya ce yana da kyau su san cewar kundin tsarin mulki bai ba su damar daukar doka a hannunsu wajen gudanar ayyukansu ba.
Kazalika, ya yi kira da su ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro a jihar don tabbatar da tsaro a fadin jihar da kewaye.
Kwamishinan ya jaddada wa al’ummar jihar aniyar rundunar na ci gaba da samar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyinsu.