’Yan Banga Sun Kashe Matasa 6 A Katsina —Fulani
Ana zargin ’yan banga da yi wa wasu matasan Fulani shida kisan gilla a yankin Matazu da ke Jihar Katsina
Jama’ar Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina na zargin ’yan banga da kisan wasu matasa shida da jikkata wasu da dama.
Ana zargin ’yan bangan sun je wata rugar Fulani ne gudanar da bincike, abin da ya yi sanadiyar kashe wasu matasa shida da jikkata wasu da ba a fadi adadin ba.
A yayin samamen ne ake zargin ’yan bangar sun ƙone rugagen Fulanin, wanda hakan ya yi sanadiyar tserewar da yawa daga cikin Fulanin.
BBC ta ruwaito wani dattijo Bafulanin Bello Shehu, yana cewa, ’yan bangar “Sun kama wasu yara maza, kuma abin takaici, sun kashe shida daga ciki.
- Gwamnatin Katsina Ta Sayo Motoci Masu Sulke Don Yaƙar ‘Yan Bindiga
- Ƙayyade Shekarun Shiga Jami’a Daidai Ne —Majalisa
“Ba mu san laifin da wadanda aka kashe suka aikata ba, mun kai rahoto ga babban jami’in ’yan sanda na yankin Matazu, kuma kwamandan soja ya ba da motar daukar gawa, an ɗauke gawarwakin.”
Bello ya ce ’yan bangar sun kai hari rugagen Fulanin ne da misalin karfe 11 na dare, inda suka razana jama’a, suka bincike gidaje, suka kona gidaje hudu, bayan sun bincike su, suka kuma kwashe dukiyoyin jama’a.
Sai dai gwamnatin jihar ta nesanta jami’an tsaronta daga zargin.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina Nasiru Muazu, ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin kuma amma tuntubar sa ya fara bincike; sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai tantance lamarin ba.
Ya ce, ya yi wa gwamnan jihar bayani, wanda ba tare da bata lokaci ba ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike da daukar matakin da ya dace.