’Yan banga sun kashe matashi da dukan kawo wuka a Zariya
A kan zargin satar waya aka kai samarin ofishin ’yan banga aka lakada musu duka sanduna
Ana zargin wasu ’yan banga da kashe wani saurayi mai shekaru 20 tare da raunata wasu biyu ta hanyar dukan kawo wuka a Anguwar Jushin Gari da ke Karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa, a ranar Juma’a ne ’yan bangan suka kama matasan a kan zargin su da satar wayar hannu, inda suka kai su ofishinsu da ke anguwar Madarkaci, Ban Zazzau kuma suka yi amfani da sanduna wajan dukan su.
Hakan ya yi sanadiyar rasuwar Abdullahi Hamza, su kuma wasu samarin biyu suka samu raunuka.
Majiyar tamu ta ce, ’yan banga da ake zargi da aikata wannan aika-aika, Ashiru Abdullahi da Kuma Tajjo, dukkansu mazauna unguwar Jushi ne.
- “An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga yayin ceto ɗaliban likitanci”
- Abin da zai hana mu biyan sabon mafi ƙarancin albashi — Inuwa
Buturen ’yan sanda Mai kula da shiyar Zariya, Kasim Abdul, ya ce tuni suka cika hannu da wadanda ake zargi da ai’kata kisan.
Jami’in ya kara da cewa rundunar ta mika wadanda ake zargin ga sashin binciken manyan laifuka da ke Kaduna domin ci gaba da bincike.
Wadanda suka samu raunuka kuma an garzaya da su zuwa Asibiti domin samun kulawa.
Kakakin Rundunar ‘yan sanda Jihar Kaduna ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce bayan sun kammala bincike za su tura wadanda ake zargin zuwa kotu.
Idan ba a manta ba, shekaru uku da su ka gabata takwarorin su da ke Kofar Doka Zariya sun taba kashe wani matashin bisa zargin satar waya.