’Yan banga sun kashe matashi kan zargin satar babur
Rundunar ’yan sandan yankin Zariya a Jihar Kaduna ta kama wasu ’yan banga uku bisa tuhumarsu da kashe wani matashi bisa zarginsa da satar babur.A watan jiya ma ’yan banga sun kashe wani matashi mai suna Umar Balele a Kwanar Shahada da ke Jushi a kan wai ya zage su. A ranar Asabar da ta […]
Rundunar ’yan sandan yankin Zariya a Jihar Kaduna ta kama wasu ’yan banga uku bisa tuhumarsu da kashe wani matashi bisa zarginsa da satar babur.
A watan jiya ma ’yan banga sun kashe wani matashi mai suna Umar Balele a Kwanar Shahada da ke Jushi a kan wai ya zage su.
A ranar Asabar da ta gabata ce ’yan sandan Samaru a karamar Hukumar Sabon Gari suka kama ’yan bangar uku da suka hada da Musbahu da Umar Ibrahim da Nasiru Yahaya bisa zarginsu da kashe matashin mai suna Hamza Yahaya da suke za rgi da satar babur a Unguwar New Edtension, Samaru.
Yayan marigayi Hamza mai suna Is’hak Sulaiman wanda ya yi magana a madadin iyalansu ya shaida wa wakilinmu cewa “A ranar Juma’a 27/9/2015 ne wasu matasa biyu cikinsu har da wani mai suna Abdulkudus sun kai karar marigayin cewa sun ajiye babur dinsu, kuma sai suka zo suka samu shi Hamza a kan babur din. Sun ce ba su yi masa magana ba, sai suka shiga wani gida, kuma bayan sun kammala abin da suke yi sun fito sai suka ga babu babur, don haka suna zargin shi ne ya sace musu babur don haka suna so a gaya masa ya dawo musu da babur dinsu. Shi ne sai mahaifiyar Hamza mai suna Malama Habiba ta ce, ta ji, in ya dawo za ta gaya masa.”
Ya ce Hamza na dawowa mahaifiyarsa ta gaya masa kuma ta yi masa fada na, sai ya fita a cikin daren, ashe wadanda suka kawo karar sun gaya wa ’yan bangar unguwar cewa, Hamza ya sace musu babur, sai suka kama shi suka ce masa ina babur?
Is’hak ya ce Hamza ya nuna musu babur ba wata gardama tare da neman su yafe masa ba zai sake ba. Kuma bayan an ga babur, sai Abdulkudus ya nemi alfarmar ’yan bangar su raka shi gidansu don ya yi wa mahaifinsa bayani, kuma da aka je wajen mahaifin mai babur ’yan bangar suka yi masa bayani, sai ya ce su saki wanda ake zargin, kuma ya ce ya yafe masa.
Ya ce sai ’yan bangar suka ce za su kai shi ofishinsu kafin su sake shi, to ashe sun tafi da shi wani waje ne suka kashe shi su ka ja shi suka kawo shi kofar masallacin saka yar.
Is’hak, ya ce da asuba jama’a sun fito Sallah sai suka ga gawar Hamza, take aka sanar wa sarki da ’yan sanda kafin a yi masa sutura.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban ’yan bangar Samaru Malam Shehu, amma lamarin ya ci tura, kuma da ya tuntubi ofishin ’yan sanda na Samaru, babban jam’insu Mannir Lawal ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce ba zai yi karin bayani ba, ya ce an kama mutanen da ake zargi tare da masu babur din za a tura su hedkwatarsu ta Kaduna don ci gaba da gudanar da bincike.