’Yan banga sun kashe tubabbun barayin shanu a Katsina
A yammacin ranar Asabar ta din makon da ya gabata ne jama’ar garin ‘Yartalata da ke cikin karamar hukumar kafur ta jihar Katsina suka ga wani abin da ba su taba gani ba, a lokacin da aka yi yunkurin yin wani taro don karbar tubar wadansu barayin shanu da suka addabi yankin. Su dai wadannan […]

A yammacin ranar Asabar ta din makon da ya gabata ne jama’ar garin ‘Yartalata da ke cikin karamar hukumar kafur ta jihar Katsina suka ga wani abin da ba su taba gani ba, a lokacin da aka yi yunkurin yin wani taro don karbar tubar wadansu barayin shanu da suka addabi yankin.
Su dai wadannan barayin shanu da suka kai akalla mutane 12,wadansu ‘Yan banga ne da ake zaton yaran wani mutun ne mai suna Isan Gona, dan karamar hukumar Bakori, wanda a lokacin rayuwarsa ya yi suna a wajen kamo irin wabannan barayi da kuma ‘yan fashi. ‘Yan Bangan, wadanda aka ce sun kai mutun 30, wadanda suke amfani da babura da kuma makaman da suka hada da sanduna adduna da sauran makamai, an ce sun yaudari wadannan mutanen ne da aka ce barayin shanu ne ta hanyar tara su waje daya bisa wata manufa, amma bayan sun taru suka kashe su.
Kamar yadda Malam Kabir Malunfashi ya shaida wa Aminiya, ya ce,’Yan nangan ana zaton na hadin gwiwa ne a tsakanin kananan hukumomin kafur da kankara da kuma Malumfashi, sune suka nemi wadannan barayi su zo su tuba kuma su rantse da Alkur’ani a kan cewa ba za su sake sata ba,sannan kuma za a ba kowannansu Naira dubu goma. Bayan wadannan barayi sun yarda da za su dauki wannan alkawari a gaban jama’a a nan garin na ‘Yartalata, a inda aka shirya wajen da za a gabatar da wannan taro, wanda har kujeru an shirya an kuma kawo Alkur’ani a aje a gabansu.
To kawai maimakon aiwatar da abin da ya kawo su, sai wadannan ‘Yan banga suka hau su da bugu. An ce faruwar hakan ya samo asali ne a kan cewa an yi musu tambayoyi ne a kan irin barnar da kowa ya aikata, inda wani a cikinsu ya ce bai san iyakar mutanen da ya kashe ba,wanda wannan furucin ne ya harzuka su suka dauki wannan matakin da ya kai ga sun kashe su.
Wata majiyar kuma ta ce,wani daga cikin barayin ne ya ce ko sun ce sun tuba karya suke yi, ‘’hakan ne ya jaza kashe su da ‘Yan bangan suka yi,” kamar yadda Malam Kabir ya shaida wa Aminiya.
Shi ma wani wanda al’amarin ya faru a gabansa ya ce, barayin su goma sha biyu suka taru kuma ‘Yan bangan duk sun kashe su kuma sun kona gawarwakinsu.
Shi kuwa wani jami’i (wanda ya nemi a sakaya sunansa da yanayin aikinsa), ya shaida wa Aminiya cewa, shine ma ya hana ‘Yan bangan kona gawar cikon mutum na sha biyun da suka dauko daga Kurmi suka kawo shi dab da shiga Malumfashi.”Na zo na tarar da har sun kashe shi sun kuma daure kan suna kokarin toya gawar wanda na hana su aiwatar da yin haka din,domin har wadansu daga cikinsu sun taso mini na ce musu su san ko wane ne za su taba? A karshe shi jagoran nasu da ake kira koshe ya ce su kyale ni, wanda hakan ya ba ni damar kwance daurin da suka yi masa. Amma bayan na baro wajen na ji an ce shi ma sun sanya masa wuta amma bai kai ga cinyewa ba danginsa suka zo suka kashe wutar suka dauki gawar. Su kuma wadancan mutane sha daya da suka kashe kuma suka kona gawarsu, bayan sun kawo su inda aka shirya za a yi wannan taro ne na tubar tasu,wadansu ma an ce ‘yan rakiya ne ba barayin ba ne, sai su ‘Yan bangan suka dauke su suka kai su cikin wani dajin da ke kan hanyar shiga garin Rugoji, inda suka kashe su kuma suka kona gawarwakin mutanen 11 da suka kai cikin wannan daji. Akwai ma wadansu mutanan biyu da suka kashe a wajen Tugen Na’alma,” inji wannan jami’in.
Shugaban karamar hukumar ta kafur Alhaji Salisu Bature dankanjiba ya nuna bacin ransa tare da yin Allah wadai da wannan mataki na daukar doka a hannu da wadannan ‘Yan banga suka dauka. Shugaban ya yi kiran da a zauna lafiya kuma a bar daukar doka a hannu bayan an san akwai jami’an tsaro.
Da Aminiya ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan sanda na jahar Katsina,Mataimakin Sufurutanda (DSP)Aminu Abubakar Sadik, ya tabbatar da faruwar lamarin,sai dai ya ce,suna nan suna cikin bincike tare da tattara bayanai, saboda an ce lamarin ya faru a cikin daji ne.
Idan za a iya tunawa dai, a shekarar bara an samu faruwar arangamomi a tsakanin barayin shanun da ‘Yan banga ko jama’ar gari a wadansu sassa na jahar Katsina, da suka hada da yankunan kananan hukumomin Batsari da Jibiya da Safana har ya zuwa su kankara da Faskari da dandume da kuma Sabuwa,wadanda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.