’Yan banga sun kashe ’yan bindiga a Kebbi

’Yan banga sun hallaka wasu ’yan bindiga uku suka addabi yankin Jihar Kebbi da yin garkuwa da mutane.

’Yan banga sun kashe ’yan bindiga a Kebbi

Wasu ‘yan banga da mafarauta. (Toshuwar ajiya).

’Yan banga sun hallaka wasu ’yan bindiga uku suka addabi yankin Ngaski da ke Jihar Kebbi da satar mutane.

’Yan bindigar sun gamu da ajalinsu a hannun ’yan banga ne a maboyarsu da ke Karamar Hukumar Ngaski ranar Alhamis.

Masu garkuwa da mutanen sun jima da addabar yankin kafin dubunsu ta cika bayan ’yan banga sun fara cafke masu yi musu leken asiri.

Darektan tsaro na jihar, AbdulRahman Usman ya ce “bayan kama masu yi wa ’yan bindigar leken asiri ne suka jagoranci ’yan banga zuwa maboyarsu da ke cikin jeji, inda aka yi musayar wuta da su,” suka ci karfinsu.

Ya bayyana jin dadinsa bisa nasarar da ’yan bangar suka samu ba tare da asarar rai ko rauni ba.

Ya kuma jinjina musu game da yadda suke taimaka wa hukumomin tsaro wajen magance matsalar tsaro a jihar.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka