…’Yan banga sun kashe ’yan uwa uku a Lambata

An zargi wasu ’yan banga da harbe wasu ’yan uwa uku da suka je cin kasuwar garin Lambata da ke karamar Hukumar Gurara ta Jihar Neja a kan babur daya. Wakilinmu ya samu labari a garin cewa matsalar ta taso ne lokacin da wani mai aikin kula da abin hawa na jihar a yankin ya […]

…’Yan banga sun kashe ’yan uwa uku a Lambata
…’Yan banga sun kashe ’yan uwa uku a Lambata

An zargi wasu ’yan banga da harbe wasu ’yan uwa uku da suka je cin kasuwar garin Lambata da ke karamar Hukumar Gurara ta Jihar Neja a kan babur daya.

Wakilinmu ya samu labari a garin cewa matsalar ta taso ne lokacin da wani mai aikin kula da abin hawa na jihar a yankin ya bukaci su tsaya, amma suka ki, inda ya bi mutanen wadanda Fulani ne masu suna Haruna Galadima da Ardo Galadima da Shu’aibu Galadima zuwa kofar kasuwar ya bukaci su ba shi makullin babur din. Sannan ya kira ’yan banga a waya, kuma da suka iso sai wani daga cikinsu ya zare bel din wandonsa ya tsala wa daya daga cikinsu ya fasa masa kai, kuma ganin haka ne dan uwansa ya zaro adda ya sare shi a hannu.
Majiyarmu ta ce ganin haka, sai daya daga cikin ’yan bangan ya harbi wanda ya yi sarar da wanda aka fasa wa kan da bindiga, inda aka tabbatar da rasuwarsu a Babban Asibitin Suleja bayan ’yan sanda sun kai su.
Wakilinmu ya samu labarin cewa, mutum na uku har ya shiga mota don komawa gida, sai ’yan bangar suka bi shi suka jawo shi daga cikin mota suka harbe shi ya mutu nan take.
Hankali ya kwanta a garin bayan masu cin kasuwar sun watse ba shiri a ranar, lamarin da ya jawo sace-sace da yin raunuka a yayin gudu, wasu kuma suka bar garin gudun ramakon gayya daga Fulanin.
Gwamnan Jihar Abubakar Sani ya ziyarci garin a ranar Litinin inda ya gana da shugabannin al’umma da na Fulani.