‘Yan banga sun kashe yaro a kan zargin satar waya a Zariya
Wani yaro dan shekara 17 da haihuwa mai suna Muhammadu Sani Aliyu ya rasu a hannun ‘yan bangar Jan Labule da ke Kofar Doka, Zariya a Jihar Kaduna, bisa zargin satar wayar hannu. Lamarin da ake zargi ya faru ne a ranar Laraba da rana bayan wani mahauci da ke sayar da nama a garejin […]
Wani yaro dan shekara 17 da haihuwa mai suna Muhammadu Sani Aliyu ya rasu a hannun ‘yan bangar Jan Labule da ke Kofar Doka, Zariya a Jihar Kaduna, bisa zargin satar wayar hannu.
Lamarin da ake zargi ya faru ne a ranar Laraba da rana bayan wani mahauci da ke sayar da nama a garejin da shi Sani da mahaifinsa suke sana’a ya ce wai Sanin ya dauke masa waya.
Bisa wannan koke da shi mahaucin ya yi, sai mahaifin yaron wanda tare suke aiki a garejin ya zaunar da dansa ya bincike shi, amma ya tabbatar masa cewa bai dauki wayar kowa ba.
Duk da haka mahaifin Sani bai gamsu ba, sai ya kira abokinsa Abubakar Umar Dan Bakano dominn ya sake bincikar sa.
- Yadda Mai Siket ‘ya yi wa tsohuwa fyade’
- Matsafa sun yi wa tsohuwa yankan rago
- Yadda ’yar shekara 34 ta haifi ’ya’ya 17 a Zariya
- Sojoji da ‘yan sanda sun ba hammata iska a Zariya
Suna cikin haka ne shi mahaucin ya kira ‘yan banga suka tafi da yaron ofishinsu da ke Kofar Doka a cikin Zariya don bincike.
”Yan banga sun hana shi shan ruwa’
Abokin mahaifin Sani ya shaida wa Aminiya cewa ko da ya bi su daga baya, yanayin da ya ga Sani babu dadi.
“Har sai da ya ce Baba Bakano ka bani ruwa in sha, amma wani daga cikin ‘yan bangan … ya ce wa marigayin kai dan ubanka ba za a baka ruwa ba, sai suka hana shi ruwan.
Bayan na dawo ne da misalin magariba sai aka kira ni cewar Sani ya rasu a ofishin ‘yan bangar Jan Labile”, inji shi abokin mahaifin yaron.
Ban san Sani da sata ba, inji mahaifiyarshi
Ita kuwa mahaifiyarsa, Malama Hannatu cewa ta yi ba ta san dan nata da sata ba.
“Don wallahi ko ranar Litinin ya tsinci kudin wata mata da ta zubar kuma da ta yi cigiya ya ba ta abunta.
“Amma in nemo magana ne to kamar fada to wannan koshakka ba bu za ta tabbata da ya yi”, a cewarta.
Mahaifiyar marigayain ta bukaci hukuma ta bi kadin mutuwar danta wanda ta ce ‘yan banga sun yi wa kusan gilla.
‘Yan sanda sun kama shugaba ‘yan banga
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya ce an kama shugaban ‘yan bangar, Abubakar Ibrahim tare da abokan aikinsa su 4.
ASP Jagile ya kara da cewa ana gudanar da bincike kuma da zarar an kammala za a tura su Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar da ke Kaduna don ci gaba da bincike.
ASP Jagile ya kara da ceaw ana gudanar da bincike kuma da zarar an kammala za a tura su Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar da ke Kaduna don ci gaba da bincike.