’Yan bangar siyasa sun kai hari a ofishin ‘yan jarida
Wasu ’yan bangar siyasar jam’iyyar APC sun kain hari a sakatariyar Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Bauch. Shigar ‘yan dabar sakatariyar ya dakatar taron ‘yan jaridar da a ciki wasu ‘yan jam’iyyar APC da suka balle ke neman a suke wasu shugabannin jam’iyyar. ’Yan bangar siyasar sun yi nasarar dakatar da harkokin […]
Wasu ’yan bangar siyasar jam’iyyar APC sun kain hari a sakatariyar Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Bauch.
Shigar ‘yan dabar sakatariyar ya dakatar taron ‘yan jaridar da a ciki wasu ‘yan jam’iyyar APC da suka balle ke neman a suke wasu shugabannin jam’iyyar.
’Yan bangar siyasar sun yi nasarar dakatar da harkokin ’yan jaridan da suke yi a sakatariyar.
Jami’an ’yan sanda karkashin jagorancin jami’in hulda da jama’ar na rundunkar ’yan sandan jihar DSP Ahmed Mohammed Wakili sun halarci sakatariya don tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai ’yan siyasar duk sun tsere daga harabar bayan isowar jami’an tsaron.
’Yan jarida biyu sun samu raunuka, shugaban kungiyar ’yan jarida na jihar Umar Sa’id tare da wasu shugabannin kungiyar sun ziyarci hedkwatar ‘yan sandan don yi bayanin abin da ya faru.