‘Yan bindigar Zamfara sun mika wuya da bayar da makamansu

Tubabbun ‘yan bindigar jihar Zamfara sun mika wuya ga gwamnatin jihar tare da mika makamansu ga rundunar ‘yan sandan jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu, ne ya sanar da hakan inda ya ce, ”Yan bindigar da suka tuba sun mika makamansu kamar: biindigogin irin na sojoji da bindigar AK 47 da wasu […]

‘Yan bindigar Zamfara sun mika wuya da bayar da makamansu

Tubabbun ‘yan bindigar jihar Zamfara sun mika wuya ga gwamnatin jihar tare da mika makamansu ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu, ne ya sanar da hakan inda ya ce, ”Yan bindigar da suka tuba sun mika makamansu kamar: biindigogin irin na sojoji da bindigar AK 47 da wasu bindigogi kirar gida da harsasai da kuma kayan sarki na sojoji. A yanzu haka sun mika bindigogin da suka kai adadi tara.

A watan Yuni na wannan shekarar ‘yan bindigar da suka tuba sun mika bindigogi biyu ga ‘yan sakai sai kuma a cikin wannan watan na Agusta wasu suka mika bindigogi uku ga ‘yan sandan jihar.