Yadda ’yan banga suka yi wa Fulani 11 ’yan gida ɗaya kisan gilla

Ana zaune ƙalau, ’yan banga suka kutsa cikin gidan Fulanin suka yi wa mutane 11 kisan gilla a cikin dare

Yadda ’yan banga suka yi wa Fulani 11 ’yan gida ɗaya kisan gilla

Gwamnatin Oyo ta fara tabbatar da mutuwar Fulani 11 ’yan gida ɗaya da ke zargin ’yan bijilante sun yi wa kisan gilla a cikin gidansu a ƙauyen Gbepakan da ke Karamar Hukumar Saki ta Yamma ta Jihar.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Reshen Jihar Oyo, Alhaji Ibrahim Jiji, ne ya jagoranci Muƙaddashin Gwamnan zuwa cikin gidan da maharan suka yi wannan ɗanyen aiki.

Ya shaida wa Aminiya cewa, “cikin daren ranar Talata da ta gabata ne wadannan ’yan bijilante suka kai hari cikin wannan gida a lokacin da mazauna gidan suke kwance suna barci inda suka kama saran su da manyan makamai har da bindiga.

“A nan take mutum 11 suka kwanta dama a yayin da wasu da yawa suke kwance a Asibitin Baptist da ke garin Saki inda likitoci suke ƙoƙarin ceton rayukansu a dalilin raunukan da suka samu.”

Da yake amsa tambaya, Shugaban Kungiyar na Miyetti Allah, ya ce, “haka kawai aka kai wa wadannan bayin Allah hari suna barci.

“Babu wata matsalar rikicin manoma da makiyaya; Haka kuma babu wani zargi na fashi da makami da ake yi wa Fulanin.

“Amma mun nemi jama’armu su yi hakuri, kada su kuskura su ɗauki doka a hannun su.

“Mun mika wannan lamari ga Allah (TWT) kuma muna jiran sakamakon da mahukumta suke yi.” inji shi.

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce ta fara bincike a kan kisan gillar da aka yi wa Fulani.

Muƙaddashin Gwamnan Jihar, Bayo Lawal, wanda yake tare da kwamishinan ’yan sandan jihar, Sonubi Ayodele, ya ziyarci ƙauyen na Gbepakan a ranar Alhamis domin gane wa idanunsa irin barnar da aka yi wa Fulanin.

Ya jajanta wa al’ummar Fulanin tare da alƙawarin yin binciken ƙwaƙwaf domin gano ainihin musabbabin kisan gillar da aka yi wa Fulanin da kama duk wanda yake da hannu domin hukunta shi.