’Yan bindiga 6 sun bakunci lahira a Bauchi

’Yan bindiga shida sun bakunci lahira bayan ’yan sanda da mafarauta suka ragargaje su a Karamar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.

’Yan bindiga 6 sun bakunci lahira a Bauchi

’Yan sanda. (Hoto: NAN)

’Yan sanda da mafarauta sun aika ’yan bindiga shida lahira bayan wani artabu a Karamar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.

’Yan sanda da mafarautan Ali Kwara sun far wa bata-garin ne a matsaysin martani kan kisan gilla da miyagun suka yi wasu mutum takwas, ciki har da basaraken kauyen Kada Gamji da ke a karamar hukumar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Auwal Musa Muhammad, ya sanar ranar Laraba a Ningi cewa a makonni biyu da suka gabata, ’yan bindiga sun kai hari a kauyukan Iyayi, Kayadda, Gamji da Bukutumbe, inda suka harbi mutum hudu, suka kashe wani dan banga a Bukutumbe.

Daga nan kuma suka tsallaka Jihar Jigawa, inda suka yi garkuwa da mata biyu na Shugaban Karaman Hukumar Kiyawa.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce bayan kisan gillar da aka yi wa mutane takwas a Ningi a watan Yuli ne rundunar ta tada wata tawagar jami’an tsaro na sirri da hadin gwiwar mafauta yaran Ali Kwara.

CP Muhammad ya bayyana cewa  rundunar hadin guiwar ta yi artabu da ’yan bindigar ne a maboyarsu da sanyin asubahin a ranar 26 ga Disamba, 2023, inda suka kashe shida daga cikinsu.

A cewarsa, jami’an sun kwato bindiga kirar AK47 guda biyu, harsashai 55, kwanson harsasai, kudi Naira miliyan 4.5, mota kirar Golf 3, sabbin layukan waya guda bakwai, da wayoyi guda shida da sauransu daga hannun ’yan bindigar.

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja