’Yan bindiga ba su da mafaka in na zama Shugaban Kasa – Atiku

Ya ce kasinsu ya bushe muddin ya zama Shugaban Kasa

’Yan bindiga ba su da mafaka in na zama Shugaban Kasa – Atiku

Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma mai neman takarar Shugaban a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ’yan bindiga ba za su sake samun mafaka ba a Najeriya muddin ya dare kujerar.

Da yake jawabi ga daliget din jam’iyyar daga Jihar Katsina ranar Laraba, Atiku ya ce tun farko sakacin Shugabanni ne ya sa bata-gari suka samu mike kafa.

Ya ce muddin aka zabe shi Shugaban Najeriya a 2023, zai tabbatar da cewa masu laifi ba su yi wani katabus ba wajen cutar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce, “Muna kan hanyar zuwa Katsina tare da tsohon Gwamnanku, Ibrahim Shema a kan jirgi, amma ba inda ba ma hangowa a kasa.

“Ina ma dajin da ake maganar ’yan bindiga na buya cikinsa da yake neman gagarar Kundila?

“Ina tabbatar muku cewa in kuka ba ni dama a 2023, batun rashin tsaro zai kasance cikin muhimman batutuwan da zan fi mayar da hankali wajen magancewa a Katsina da ma Najeriya baki daya,” inji Atiku.

Daga nan dan takarar ya bayyana wuraren da zai fi mayar da hankali da suka hada da hadin kan kasa da tattalin arziki da ilimi da kuma sauya fasalin kasa ta hanyar kara wa Jihohi karfin iko.

Daga cikin ’yan tawagar Atikun yayin ziyarar akwai mamallakin gidan talabijin na AIT, Cif Raymond Dokpesi da Sanata Baraka Sani da Sanata Abdul Ningi da Alhaji Adamu Maina Waziri da kuma tsohon Sakataren PDP na kasa, Umar Tsauri.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno