’Yan bindiga biyar ne jama’a suka kashe a kauyen Kaduna

A ranar Lahadin da ta gabata ce dubun wasu da ake zargi da yawan sace shanun jama’a ya cika a kauyen Fadan Kaje da ke karamar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna inda mutanen garin suka aika da su Lahira bayan sun kai hari kauyen. Rahotanni daga yankin sun ce barayin shanu masu dauke […]

’Yan bindiga biyar ne jama’a suka kashe a kauyen Kaduna

M.D Abubakar, Sufeto Janar na ‘Yan sandan NajeriyaA ranar Lahadin da ta gabata ce dubun wasu da ake zargi da yawan sace shanun jama’a ya cika a kauyen Fadan Kaje da ke karamar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna inda mutanen garin suka aika da su Lahira bayan sun kai hari kauyen.
Rahotanni daga yankin sun ce barayin shanu masu dauke da bidigogi sun dade suna addabar mutanen yankin ta hanyar kai masu hari da daddare suna kashe mutane a wasu lokutan su banka wa gidajensu wuta.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa a wannan rana mutanen garin sun yi ta maza sun tunkari ’yan bindigar bayan sun zo kauyen kuma na take al’ummar garin suka halaka mahara biyar.
Majiyar ta ce wasu daga cikin mutanen kauyen sun samu raunuka a lokacin artabu maharan.
Wani jami’in tsaro da ba ya son a bayyana sunansa, ya ce suna ci gaba da bincike domin gano ko su wane ne maharan kuma mene ne manufarsu.
“Muna bincike a yankin amma hakikanin zancen ne akalla mutum biyar daga cikin maharan ne suka mutu, kuma mutanen kauyen ne suka kashe su.  Wannan shi ne karon farko da mutanen gari suka yi nasarar halaka maharan da suka dade suna kai masu hari tare da kashe musu jama’a,” inji shi.
Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun kashe mutum uku kafin a fi karfinsu a aika da su barzahu, a fafatawar da aka dauki sa’o’i ana yi a tsakanin banagrorin biyu.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Olufemi Adenaike ya tabbatar da kai harin ta wayar tarho inda ya ce tuni ’yan sanda suka isa yankin da nufin gano maboyar maharan.
Ya yi kira ga mutanen yankin su taimaka musu da bayanai sahihai da za su kai ga gano saura da maboyar mahara a yankin.