‘Yan bindiga: Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi

Jihohin Arewacin Najeriya sun amince su yi aki tare domin yakar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a yankin. Gwamnonin jihohin Arewa maso yamma da takwaransu na jihar Neja sun amince su yi taron dangi wajen magance musamman matsalar ‘yan fashin daji. Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana haka bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu […]

‘Yan bindiga: Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi

‘Yan bindiga sun kashe basarake a jihar Kebbi

Jihohin Arewacin Najeriya sun amince su yi aki tare domin yakar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a yankin.

Gwamnonin jihohin Arewa maso yamma da takwaransu na jihar Neja sun amince su yi taron dangi wajen magance musamman matsalar ‘yan fashin daji.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana haka bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari kan matsalar tsaron da ke addabar jiharsa.

Tambuwal ya ziyarci shugaban ne domin neman karin dauki sakamakon harin ‘yan bindiga da suka hallaka mutum 60 a Karamar Hukumar Sabon Birni.

Gwamnan ya nemi a tura karin jami’an tsaro domin magance matsalar maharan da ke zubar da jinin jama’arsa.

Ya kuma nemi daukin Gwamantin Tarayya ga ‘yan jihar da ke gudun hijira sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

“Bayan hare-haren baya, kwana biyu da suka wuce ‘yan fashin daji sun hallaka mana kusan mutum 74 a harin da suka kai.

“Na yi wa shugaban kasa cikakken bayani tare da gabatar masa irin taimakon da mu da jami’an tsaro ke nema domin tababtar da tsaro,” a cewarsa.

A ranar Alhamis ne Shugaba Buhari ya umarci sojoji da su murkushe ‘yan ta’addan da ke addabar jihar Sokoto.