’Yan bindiga: Har yanzu Janar Tsiga na tsare bayan kwanaki 29

An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna garin su tara,

’Yan bindiga: Har yanzu Janar Tsiga na tsare bayan kwanaki 29

Kwanaki 29 ke nan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutane.

An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna garin su tara, a wata ranar Laraba.

Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan Janar ɗin da aka sace domin neman kuɗin fansa na Naira miliyan 250m.

Wata majiya ta kusa da dangin ta shaida wa wakilinmu cewa, har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da nufin ceto Janar ɗin sojan mai ritaya.

“Abin takaici ne yadda har yanzu Janar ɗin da sauran waɗanda suka yi garkuwa da su suna hannun waɗanda suka sace su a cikin wannan wata na Ramadan.

“Zan iya tabbatar muku da cewa ana tattaunawa, kuma addu’o’inmu na tare da shi da duk sauran waɗanda abin ya shafa da ke tsare,” in ji majiyar.

Wata majiyar kuma na kusa da dangin, ta bayyana fargabar yin magana da manema labarai, inda ta ce bisa ga bayanan da aka yi ta yaɗa jita-jita game da sace Janar ɗin, zai yi musu wuya su ce komai ga ‘yan jarida.

Sai dai ya tabbatar da wata majiya na cewa ana ci gaba da tattaunawa don ganin an sako Janar ɗin.

A halin da ake ciki, rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta ce, ana ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar tarayya da ke Dutsin-Ma da aka sace.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya ce rundunar ’yan sandan tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro na ƙoƙarin kuɓutar da wandanda aka sace tare da kamo masu laifin.