’Yan bindiga na farautar mu kusan kullum —Sarkin Zazzau
Yadda ’yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin Zariya.
Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan yawaitar ayyukan ta’addanci a masarautarsa inda ya ce ’yan bindigar sun mamaye masarautar ta yadda suke farautar mutane a kusan kullum.
Sarkin ya ce duk da cibiyoyin soja da ke Zariya, masu garkuwa da mutanen sun mamaye hatta kewayen birnin.
Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Tsaro na Jihar, Mista Samuel Aruwan ya jagoranci manyan jami’an tsaron da ke jihar don jajanta wa Sarkin bisa hare-haren da ake kaiwa a birnin na Zariya a ’yan kwanakin nan.
Shugabannin tsaron sun kai ziyarar ce bayan ’yan bindiga sun sace dalibai kai hari Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, suka kashe dalibi, suka harbi wani, sannan suka yi awon gaba da dalibai takwas da malamai biyu.
Sarki Ahmad Bamalli ya ce hare-hare suna faruwa kusan a kowace rana a tsawon makon jiya.
Ya ce idan Zariya mai manyan cibiyoyin tsaro za ta zamto karamar danga ga masu garkuwa da mutane, to hakan yana nuna tsarin tsaron kasar nan yana cikin babbar matsala.
Sarkin ya lissafo cibiyoyin tsaro na soji da ’yan sandan kasa da na sama da suke jihar, inda ya ce idan har Zariya a matsayin mazaunin masarautar za ta ci gaba da fuskantar rashin tsaro, to, lamarin zai shafi daukacin Arewa domin hanyar ce take hada da Arewa da sauran sassan kasar nan.
’Yan bindiga sun sace mutum 12 a Zariya
Kain harin kwalejin, ’yan bindigar sun kai hari wurare daban-daban a Zariya a daren Asabar da ta wuce inda suka sace mutum 12 a sabuwar unguwar da ke tsakanin Kofar Gayan da Kofar Kona a Zariya.
Wata ganau, kuma ’yar daya daga cikin mutanen da aka sace, Hafsat Dokta Habib Kusfa, ta ce ’yan bindigar sun shiga gidansu ne da misalin karfe 12:00 na dare suka bi daki-daki suna fito da mutane suna jera su a tsakar gida.
Hafsat ta ce sun shiga gidan dauke da bindigogi da adduna suna magana da Fulatanci da Hausa.
Yadda ’yan bindiga suke sukuwa a kan mutanen Zariya
Ta ce bayan gardama a tsakaninsu, ’yan bindigar sun ce ta koma gida ta kula da kananan yara da kishiyar mahaifiyarta da take jego.
“Sun tafi da mahaifina, Dokta Habib Kusfa da mahaifiyata da kannena da ’yan uwana, sun tafi da mutum takwas daga gidanmu.
“Mun kuma ga wadansu ’yan bindigar sun fito da wadansu mutane galibi maza daga gidajen makwabta inda suka tafi da su.
“’Yan bindiga bakwai ne suka shiga gidanmu, kuma biyu daga cikinsu suka tsaya a waje, ba su wuce shekara 15-30 ba,” inji Hafsat.
Hafsat ta ce, ’yan bindigar sun sako mahaifinta da mahaifiyarta a ranar Lahadi da safe inda aka kai su asibiti saboda ba sa iya magana.
Ta ce lokacin da suka dawo alamu sun nuna cewa sun sha duka a wurin ’yan bindigar.
Wasu rahotanni sun ce ’yan bindigar sun sace wani tsohon manajan banki a gidansa da ke Unguwar Giresland a Kwangila, Zariya da karfe 9:00 na dare ranar Juma’a.
Bala’in ya sa Musulmi sun koma ga Allah
Sakamakon jerin hare-haren da ’yan bindiga suke kaiwa a sassan Zariya suna sace mutane, wadansu malaman addinin Musulunci a Karamar Hukumar Zariya sun gudanar da Sallar Salatul Haja tare da Alkunutu domin rokon Allah Ya kawo dauki kan abin da yake faruwa a yankin.
Malam Tanimu Abubakar Mai Rawani, da ya daga cikin wadanda suka shirya sallolin, ya ce yin wannan ibada ya zama wajibi a irin wannan lokaci saboda Sunnah ce ta Manzon Allah (SAW) duk lokacin da abu yake faruwa mutane su kaskantar da kai su koma bayan gari domin addu’o’i da neman Allah Ya kawo dauki.
Ya ce mutanen Zariya suna cikin tsaka-mai-wuya kuma ba su iya barci, saboda matsalar tsaro na neman fin karfin gwamanti.
Malam Tanimu Mai Rawani, ya ce suna sa ran da wannan insha Allah batun ayyukan ta’adanci ya zo karshe a Najeriya.
Da yake bayani bayan kammala addu’o’in, Sheikh Malam Habibu Usman ya ce, ta’adanci irin na masu garkuwa da mutane ya saba wa koyarwar addini.
Don haka, wajibi ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan matsala.
Shi kuwa Garkuwan Makarantar Zazzau Alhaji Shamsuddin Aliyu, ya ce lokaci ya yi da za a bar mutane su dauki matakin kare kansu, saboda a zahiri gwamnati ta gaza.
Ya ce dole jama’a su koma ga Allah kowa ya gyara zuciyarsa idan aka yi haka ana sa ran za a samu mafita.
Garkuwan Makarantar Zazzau ya ce jarrabawar biyu jama’a ke fama da ita, akwai na gwamnati da na masu garkuwa da mutane.
Ya ce korar ma’aikata da Gwamnati ke yi ba gaira ba dalili yana sabbaba karuwar marasa aikin yi.
Sai ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai su samar wa matasa aikin yi domin rage zaman kashe wando da ake fama da shi.
’Tun da aka sako ’yan bindiga 5 muka shiga uku’
Mutanen yankin Zariya sun dora alhakin ta’azzarar hare-haren ’yan bindiga a kan sako wadansu masu garkuwa da mutane su biyar da suke zargin ’yan sanda sun yi a ranar 31 ga Mayun da ya gabata, bayan ’yan banga sun kama su sun mika wa ’yan sandan a watannin baya.
Mazauna yankin sun ce ana sako ’yan bindigar sai harkokin tsaro suka tabarbare a yankin, bayan sun samu saukin haka a lokacin da aka kama mutanen.
Mutanen yankin da Aminiya ta tattauna da su da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce a mako biyu da suka gabata ’yan bindigar sun rika tsare hanyar Kaduna zuwa Zariya a-kai-a-kai suna fashi da sace mutane har lamarin yake kokarin cim ma birnin Zariya da kewaye.
Sun ce an fara kai harin ne a ranar 3 ga Yuni a Dumbin Rauga, dab da Kamfanin Taki na MATRID a hanyar Kaduna zuwa Zariya.
Sai kuma washe-gari Juma’a 4 ga Yuni ’yan bindigar sun tare hanyar suka bude wa wata motar fasinja wuta suka kashe mutum biyu suka raunata biyar.
A ranar Alhamis din makon jiya kuma, da misalin karfe 1:00 na dare, ’yan bindigar suka sake tsare hanyar Kaduna, daidai Dumbin Rauga, daga baya suka ratsa ta cikin Dumbin Rauga da ke Gundumar Dutsen Abba suka shiga gida-gida, har da na Hakimin garin, Alhaji Falalu Usman, Maharin Zazzau.
Maharan sun kuma sun sace mata bakwai a unguwar, cikinsu har da wata mai tsohon ciki mai suna Adasiya da yara ’yan mata biyar da karamin yaro.
’Yan bindigar da aka sako
’Yan bindigar da aka sako a ranar Litinin 31 ga Mayu, a baya ’yan kungiyar sa-kai ne suka kama su bisa zargin su da kai hare-hare a Gundumar Dutsen Abba da kewaye.
Garuruwa da kauyukan da suke fuskantar sabuwar barazanar tsaro a yanzu su ne Unguwar Malam Atiku da Tankarau da Kamfanin Saye da Unguwar Kanawa da Majeru da Sabon Garin Kugu da Sabon Gida da Kasuwar Dutse da Unguwar Dallatu da Kafin Fulani da Mardanni da Rafin Yashi zuwa Kwaba.
Sai kuma yankin Dorayi da Buzai da ke Kofar Gayan da Dumbin Rauga, kafin lamarin ya danna zuwa dab da birnin Zariya.
Mutanen yankin sun ce tun da aka sako wadanda ake zargin, rashin tsaro ya sake dawowa fiye da baya a yankin Dutsen Abba da kewaye.
Kungiyar ’yan sintiri ta KADBS ce dai ta kama mutum shida da ake zargin da kai hare-hare da kashe mutane da garkuwa da mutane a yankin Dutsen Abba.
Aminiya ta ruwaito a ranar 4 ga Fabrairun 2021 cewa da misalin karfe 11:00 na dare wadanda ake zargin tare da wadansu da ba a kama su ba dauke da bindigogi kirar AK 47 suka auka wa kauyen Unguwar Hazo da ke Gundumar Dutsen Abba, inda suka kashe wani mai suna Musa Isa dan shekara 28 da Yusuf Sulaiman mai shekara 30.
Maharan sun harbi matan aure biyu masu suna Fatima Sulaiman (Magajiya) mai shekara 64 da Hafsatu Isa (Uwa) mai shekara 50.
Sun kuma kwace babura kirar ‘Boxer’ guda hudu, kuma sun kai hari gidan Kansilan Dutsen Abba, Alhaji Abdul’aziz Sani, a Unguwar Makada inda suka sace matarsa Samira Abdul’aziz da wata matar aure mai suna Halima M. Sani.
Bayan harin ne ’yan Kungiyar Sintiri ta Jihar Kaduna da ke Unguwar Mai Turmi a Karamar Hukumar Igabi suka tsare masu garkuwar inda suka ceto wadanda aka sato da kuma kwato baburan hudu.
Kungiyar ta kama Mu’azu Sani wanda kanen Kansilan ne da Mubarak Adamu da ke Unguwar Makada da Faisal Shehu, wani Bafulatani mazaunin Unguwar Malam Atiku da Yunusa Audi da Sani Igwa da kuma Abubakar Muhammad, wadanda aka mika su ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna don ci gaba da bincike da tabbatar da an hukunta su, amma sai ’yan sandan suka sako su.
Kansilan Dutsen Abba Alhaji Abdul’aziz Sani, ya tabbatar wa Aminiya cewa an sako wadanda ake zargin, ya ce daga cikin mutum shida da aka kama, kanensa ne kawai ba a sako ba.
Ya ce, ganin wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu da kansu a gaban al’ummar yankin, kuma an samu wadansunsu da makamai, sakinsu ya ba jama’a mamaki.
Abdul’aziz ya ce bayan da aka kama su, yankin ya samu saukin irin wannan ta’addanci.
Sai ya nuna damuwa a kan sake tabarbarewar tsaro bayan sako su, inda ya ce al’amuran tsaro sun sake sukurkucewa a yankin.
A don haka al’ummarsu suna cikin damuwa, a daidai wannan lokaci da suke shirin fara aikin gona.
Kasilan ya ce rashin tsaro na iya hana manoman yankin da baki masu zuwa gudanar da aikin gona a bana.
Za ku ji dalilin sakin masu garkuwar – ’Yan sanda
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige, kan sako wadanda ake zargin, sai ya nemi ta ba shi sunayen wadanda aka sako din.
Bayan aike masa da sunayen, ya kira inda ya tabbatar da cewa ya karbi sunayen kuma ya yi alkawarin zai kira don ya yi bayanin dalilan da suka sa aka sako su.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai ba da bayani a kan dalilan sako wadanda ake zargin ba.
ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar harin sai dai ya ce ba su san yawan mutanen da ’yan bindigar suka sace ba.
Ya ce suna tattara bayanan lamarin da wadanda abin ya shafa.