’Yan bindiga na neman N16m da 4 babur kan mutane 11 a Kaduna
‘Yan bindigar sun kai harin ne cikin daren ranar Asabar.
’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 11 a kauyen Kubuwo da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, inda suka bukaci Naira miliyan 16 da sabbin babura hudu a matsayin fansa.
Aminiya ta gano cewa Kubuwo kusa da kauyen Kudiri, inda mutanen kauyen suka tsare duk da cewa an biya kudin fansa miliyan 10.
- Zaben Adamawa: Hudu Ari ya yanke jiki gabanin gurfanar da shi a kotu
- Yadda Za Ku Gane Kayan Abinci Marasa Inganci Nan Take
Wani mazaunin garin Kubuwo, Alkali Danjuma, ya ce ranar Asabar da dare ne ’yan bindigar suka mamaye kauyen “a kan babura suna harbi a iska, wasu daga cikinsu suka shiga gidaje uku suka kwashe mutum 11 ciki har da yara uku.”
Ya ce shugaban ’yan bindigar ya kira waya da yammacin Lahadi suna neman kudin fansa da babura hudu daga ’yan uwan wadanda abin ya shafa.
Shugaban kauyen Kudirida ke kusa da su, Wakili Iliya, ya ce “da misalin karfe 2 na safiyar yau na samu kira cewar ’yan bindiga sun mamaye Kubuwo kuma sun yi awon gaba da wasu mutane.”
Ya roki gwamnati da ta kawo musu dauki wajen ceto wadanda aka sace a kauyensu.
Babu wani martani a hukumance daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna kan lamarin.