’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina

Abdulsalam da mahaifinsa da ɗan uwansa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, suna nan da ransu a hannun ’yan bindiga, ba a kashe su ba.

’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina

‘Yan bindiga

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani gwarzon musabaƙar karatun Al-Qur’ani a Jihar Katsina, Abdulsalam Rabi’u Faskari, suna neman naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, Kwamishinan watsa labarai da al’adu na Katsina, Bala Salisu-Zango ya ce Abdulsalam da mahaifinsa da ɗan uwansa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, suna nan da ransu a hannun ’yan bindiga, ba a kashe su ba.

Ya ce “Gwamnati ta samu labarin wani saƙon jaje da ake yaɗawa wanda mai ba gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin watsa labarai ya sa wa hannu, wanda ke nuna cewa ƴanbindiga sun kashe gwarzon musabakar karatun Al-Qur’ani na Najeriya, Abdussalam Rabiu-Faskari.

“Muna godiya da kulawar gwamnatin Kebbi, amma muna bayyana wa duniya cewa Rabiu-Faskari da mahaifinsa da ɗan uwansa suna nan da ransu cikin ƙoshin lafiya a hannun ’yan bindigar.”

Salisu-Zango ya ƙara da cewa ’yan bindigar suna neman kuɗin fansa har naira miliyan 30 ne domin sako mutanen.

Ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin ceto su, tare da tabbatar da cewa sun koma gida lafiya, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar na ƙoƙari matuƙa domin magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yammacin ranar Talatar da ta gabata ce ’yan bindigar suka sace mutanen a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Jihar Kebbi.

Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, shi ne ya zo na ɗaya a musabaƙar a ɓangaren maza.