’Yan bindiga na tserewa zuwa cikin al’umma a Sakkwato —Gwamnati

Gwamnatin Sakkwato ta gargaɗi al’ummar jihar cewa su yi hattara da ’yan bindiga da ke tserewa a sakamakon tsananta ragargazar da sojoji suka tsananta a kansu.

’Yan bindiga na tserewa zuwa cikin al’umma a Sakkwato —Gwamnati

Gwamnatin Sakkwato ta gargaɗi al’ummar jihar mazauna kan iyakoki da su yi hattara da ’yan bindiga da ke tserewa a sakamakon ragargazar da sojoji suka tsananta a kansu.

Hakan na zuwa ne a yayin da hare-haren da sojoji suka tsananta suka kai ga kashe manyan kwamnadojin ƙasurgumin ɗan ta’adda Bello Turji, guda bakwai da kuma mataimakinsa.

Mashawarcin Gwamna Ahmad Aliyu kan sha’anin tsaro, Ahmad Usman ya sanar a ranar Laraba cewa ragargazar da sojoji ke wa ’yan bindiga a yankin Gabashin Sakkwato da kewaye na samun gagarumar nasara tare da gigita ’yan ta’addan, “inda aka tarwatsa maɓoyansu.

“Sojoji sun kuma kashe ’yan ta’adda masu yawa, kuma suna ci gaba da ceto ɗaruruwan mutanen da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

“Tsananta ragargazar ’yan bindigar da aka yi ta sa sun ranta a na kare zuwa wasu wurare da raunukan harbi da ke jikinsu.

“Don haka jama’a su yi hattara, domin ’yan bindigar na iya bayar da kamanni su shiga yankunansu domin yin jinyar raunukan nasu a asibitocin yankunan,” in ji Usman.

Ya kuma buƙace su da su kai wa jami’an tsaro rahoton duk baƙon da ba su aminta da shi ba, yana mai jaddada cewa Gwamantin Jihar  Sakkwato za ta ci gaba da ba wa hukumomin tsaro haɗin kan da ya kamata domin wanzar da tsaro da zaman lafiya a jihar.