’Yan bindiga sun ƙone ofishin ’yan sanda da bam a Anambra

Maharan sun hallaka jami’an ‘yan sanda biyu da ke bakin aiki a yayin harin.

’Yan bindiga sun ƙone ofishin ’yan sanda da bam a Anambra

Wasu ’Yan Bindiga sun ƙone ofishin ’Yan Sanda na yankin Umunze da ke Ƙaramar Hukumar Orumba ta Kudu a Jihar Anambra, tare da kashe jami’an ’yan sanda biyu.

Masu harin sun yi amfani da bama-bamai da bindigogi, wanda ya haddasa gobara a wani ɓangare na ofishin.

A lokacin harin, ’yan sanda biyu da ke bakin aiki sun rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin kare ofishin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar harin.

Ya ce an kwashe gawarwakin jami’an da suka rasu zuwa ɗakin ajiye gawa.

Ya ce an tura dakarun tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji don bin sahun ’yan bindigar.

Kazalika, ya ce sun gano bama-bamai guda biyar da ba su tashi ba a yayin harin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Nnaghe Obono Itam, ya ziyarci wajen domin duba halin da ake ciki tare da tabbatar da tsaro.

Ya yi kira ga duk wanda ke da bayanai da za su taimaka wajen kama waɗanda suka kai hari.

Ya ce rundunar za ta tabbatar ta kama masu laifin tare da gurfanar da su.