’Yan bindiga sun bukaci N900m kudin fansar mutane 13 da suka sace a Abuja
Sun sace fasto da mace mai juna biyu da kasarake da malamin makaranta
’Yan bindiga sun bukaci a biya su Naira miliyan 900 a matsayin kundin fansa kan wasu mutane 13 da suka sace a Abuja.
Da tsakar daren Litinin ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da mutanen su 13 a unguwar Piko da ke Karamar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa a wadanda aka yi garkuwa da su har da mace mai juna biyu da wani basarake da fasto da kuma malamin makarantar firamaren gwamnati.
Ya ce da zuwan ’yan bindigar suka wuce kai-tsaye zuwa wata rugar Fulani inda suka tasa keyar mai juna biyun da wasu makiyaya biyu.
- Sojojin Nijar sun kama jagoran ’yan bindigar Najeriya
- Mun ba Tinubu sa’o’i 48 ya soke harajin tura kudi ta intanet —SERAP
Bayan harin ne ’yan bindigar suka kira suna neman a biya su kudin fansa Naira miliyan 900 da sauran abubuwa kafin su sako mutanen.
Amma shaidan ya ce daga bisani masu garkuwar sun sako mai juna biyun da basaraken da malamin makarantar wanda nakasasshe ne da kuma karin mutum guda.
Wakilinmu ya nemi karin bayani daga hukuma, amma kakakin ’yan sandan birnin tarayya, Josephine Adeh, ta ce za ta bincika, sannan daga baya ta yi bayani.
Sai dai kuma hakan bai samu ba, har zuwa lokacin da muka kammala wannan labarin.