’Yan bindiga sun dawo hanyar Abuja-Kaduna, sun sace matafiya 30

Bayan samun lafiya na tsawon wata 10 a hanyar ’yan bindiga sun sake dawowa.

’Yan bindiga sun dawo hanyar Abuja-Kaduna, sun sace matafiya 30

’Yan bindiga sun sace matafiya 30 a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. 

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a Dogon-Fili kusa da Katari a Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Karo na farko ke nan cikin fiye da wata 10 da mahara suka sace jama’a a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Binciken Aminiya ya nuna cewa hari na karshe da aka kai a kan titin shi ne na ranar 1 ga watan Maris, 2023, wanda da aka sace mutum 23.

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya sanar a shafinsa na X cewa abokansa biyu daga ’yan siyasa sun tsallake rijiya da baya a harin na ranar Lahadi.

Ya ce ’yan bindigar sun ci karensu babu babbaka na tsawon lokaci duk da cewa an girke jami’an tsaro a kan babar hanyar.

Shehu Sani ya ce, “A daidai lokacin da muke tunanin mun samu kwanciyar hankali, a daren jiya (Lahadi) ’yan bindiga sun kai hari, sun dawo hanyar Kaduna-Abuja.

“Sun tare hanyar da misalin karfe 9 na dare inda suka sace mutane masu yawa a kusa da kauyen Katari.

“Abokaina biyu, dan jam’iyya mai mulki da dan adawa sun tsere daji kamar Usain Bolt.

“Amma duk da an inganta tsaro a kan hanyar fiye da yadda yake a baya.”

Wani mazaunin Katari, Suleiman Dan Baba, ya ce da misalin karfe 9:33 na dare ne ’yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 suka fito daga daji suka tare kowane bangaren titin kuma sun dauki tsawon minti 45 a kan hanyar.

Suleiman ya ce maharan sun bude wa motocin matafiya wuta, suka fasa musu tayoyi, wanda hakan ya sa dole suka tsaya.

“’Yan bindigar sun tilasta wa matafiya fita daga motocinsu da bakin bindiga, suka wuce da su cikin daji,” in ji shi.

Wani mazaunin garin Jere, Samaila Shehu, ya ce lamarin ya faru ne da nisan kimanin kilomita daya daga garinsu, kuma an sace matafiya sama da 30 a wurin.

Yadda abin ya faru

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun raba kan su gida biyu, inda daya tsagin suka kai farmaki kauyukan Bishini da Kokore da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, daya tsagin kuma suka yi awon gaba da matafiya da ba a tantance adadinsu ba.

Wani shugaba a yankin Jere, Shu’aibu Adamu Jere, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa dan uwansa ya kubuta daga harin na kusa da Katari a ranar Lahadi.

Ya ce an jikkata wani direba, sannan an gano motoci biyu, kirar Sharon da wata karamar mota a bakin hanya babu kowa a cikinsu bayan harin.

“Eh, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na dare, kuma sun dauki tsawon minti 45 a kusa da Dogon Fili da ke kusa da Katari a ranar Lahadi.

“An harbi wani direban daya daga cikin motocin kuma aka bar shi a wurin. Akwia wani dan uwana da ya tsira daga harin,” in ji shi.

Sai dai ya kasa bayyana adadin mutanen da aka sace a harin, amma ya ce an garzaya da direban da ya jikkata zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin yi masa magani.

Shi ma wani mazaunin Katari, wanda lauya ne amma ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa an tare hanyar a daren Lahadi a lokacin da yake shirin komawa Kaduna.

A cewarsa, sojojin da ke da nisan mil 500 daga Katari sun fatattaki ’yan bindigar.

“An fada min cewa ’yan bindiga sun tare hanya a daren kafin sojoji da ke Katari su zo zu fatattake su. Amma ban sani ba ko an sace mutane,” in ji shi.

Da aka tuntubi kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba.

Shi ma kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, da aka tuntube shi, ya ce zai bincika dom tabbatar da gaskiyar lamarin.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa