’Yan bindiga sun fara karbar haraji a Sabon Birni
’Yan bindiga sun sanya wa al’ummar kauyukan da ke yankin Karamar Hukumar Sabon Birni harajin da za su rika biya domin su zauna lafiya. Duk da irin matakan da gwamnati take dauka na kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, amma har yanzu ana ganin ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka. Najeriya A […]
’Yan bindiga sun sanya wa al’ummar kauyukan da ke yankin Karamar Hukumar Sabon Birni harajin da za su rika biya domin su zauna lafiya.
Duk da irin matakan da gwamnati take dauka na kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, amma har yanzu ana ganin ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka.
- Najeriya A Yau: Dalilan da ke jawo hauhawar farashin kayan masarufi
- An kara wa’adin hade layin waya da lambar NIN zuwa karshen 2021
Wani rahoton da ya fito daga yankin Sabon Birni ya bayyana yadda ’yan ta’adda kan kai hari a kowane lokaci suka ga dama, su sace wanda suka ga dama su kashe wanda kwanansu ya kare.
Wani dan asalin yankin mazaunin Jihar Neja, ya aikewa da wakilin Aminiya cewa ko a makon da ya gabata ’yan bindiga sun aika musu takardu dauke da sakon za su kai hari a wasu kauyuka da suka hada da Hawan Diram, Dan marke da Dakwaro.
Sauran sun hadar da Kwarangamba, Teke, Kwatsal da kuma Katuma kuma wadannan kauyuka basu da wani zabi da ya wuce hada kudaden tare da mika masu.
“Wannan duk yana zuwa ne bayan an hana mu noma, an sace dabbobinmu , yanzu ina akeso mu saka kan mu, talauci ya addabemu ga kuma ’yan ta’adda” cewar wani wanda abin ya shafa.
Daga karshe ya yi kira da gwamnati ta kara kaimi kan irin kokarin da take yi na ganin kawo karshen wannan rikici da ya addabi yankin.