’Yan bindiga sun fille kan dan tauri a Kaduna

’Yan ta’adda sun  fille kan dan taurin mai suna Garba Sarki ne bayan sun jima suna bibiyar sa.

’Yan bindiga sun fille kan dan tauri a Kaduna

‘Yan banga

’Yan bindiga sun fille kan wani dan tauri a kauyen Dogon-Daji da ke Karamar Hukumar Kargo a Jihar Kaduna.

Wani shugaban al’ummar yankin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun  fille kan dan taurin mai suna Garba Sarki ne bayan sun jima suna bibiyar sa.

Ya ci gaba da cewa ’yan bindigar sun kullaci Garba Sarki ne tun bayan wani artabu da ya yi da su a daji inda ya kashe biyu daga cikinsu a watannin baya.

A cewarsa, daga bisani suka sake yin karon batta, inda ’yan bindigar suka bude wa dan taurin wuta ammaba ta kama shi ba.

Ganin haka ne suka yi taron dangi suka kama shind karfin tsiya suka daure, suka yi masa ya kan rago.

Ya kara da cewa an yi wa Garba Sarki wannan kisan gilla ne a cikin daren Alhamis a cikin dokar daji.

Shugaban al’ummar ya ce sai ranar Asabar aka gano gawar mamacin inda aka tura ’yan banga suka dauko ta aka sallace ta.

Wani dan banga a yankin mai suna Haruna ya ce, mamacin “ya dade yana ragargazar ’yan bindiga a yakin, a kwanakin baya ma ya kashe ’yan bindiga biyu.”

Kokarin wakilinmu na  samun karin haske kan wannan lamari daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna,  ASP Hassan Mansur bai yi nasara ba.

Jami’in hulda da jama’an bai amsa kiran da aka yi masa ba har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan labari.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya