’Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Argungu

Al’ummar garin Argungu da ke Jihar Kebbi sun kwana a ranar Alhamis din makon jiya cikin dar-dar bayan da wasu ’yan bindiga suka kai wa garin hari suka yi harbe-harbe na tsawon sa’a daya a unguwanni daban-daban.Harin ya ci rayukan dan sanda daya mai suna Saje Umaru Bala Sanyinna da Alhaji Isah Abdullahi dan Tagago […]

’Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Argungu

Al’ummar garin Argungu da ke Jihar Kebbi sun kwana a ranar Alhamis din makon jiya cikin dar-dar bayan da wasu ’yan bindiga suka kai wa garin hari suka yi harbe-harbe na tsawon sa’a daya a unguwanni daban-daban.
Harin ya ci rayukan dan sanda daya mai suna Saje Umaru Bala Sanyinna da Alhaji Isah Abdullahi dan Tagago Ma’ajin Yankin Raya kasa na Gulma/Lailaba, a yayin da mutum hudu da suka hada da Haliru Isah da Muhammadu Marina da Suleman Yusuf Na-Ingila da Muhammed Adamu  (danzabarma) suke kwance a asibiti sakamakon raunukan harbin bindiga da suka samu.
daya daga cikin majinyatan Malam Muhammadu Marina ya shaida wa wakilinmu cewa, “Muna zaune a Unguwar ’Yar Dole mu uku da misalin karfe 7:30 na yamma sai muka ji karar harbi, kuma a daidai wannan lokacin na je wani shago sayen ruwa, ina tsaye daga nan ban san komai ba kawai sai na ga kaina a gadon asibiti.”
Shi kuwa danzabarma da harin ya rutsa da shi ne a Unguwar Dogo-Ka-Fi-Mari ya ce yana zaune a kan benci kawai sai ya ji wani abu ya wuce ta gefen kunnensa, kuma sai ya ji harbi a cinyarsa.
Na-Ingila wanda ya ce a gabansa aka harbe marigayi Saje Umaru ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin abokansa sun fada magudanar ruwa ne suka buya shi kuma sai ya rude ya nufi inda masu harbin suke, sai dai Allah Ya kiyaye harsashin ya same shi ne a hannun hagu.
Shi kuwa Haliru Isa wanda abin ya same shi ne a wajen da aka kama dan bindigar ne ya ce yana hanyarsa ta zuwa bariki a hanyar Sakkwato a kan babur da abokinsa sun iso daidai gidan man dan Farashi sai ya ji harbi daga nan ya yar da babur ya fadi.
Mataimakin shugaban asibitin Argungu Malam Muhammed Bello ya tabbatar da kai musu gawar dan sandan da Isah dan Tagago da kuma mutum hudu da aka harba, kuma ya ce sun yi tsayar da zubar jini kafin a yi hoto don tabbatar da akwai harsashi a cikin jikinsu ko kuma babu.
Wani dan acaba da ya nemi a sakaya sunansa wanda tun daga inda ’yan bindigar suka fara bude wuta da aka yi ihu yake bin su har inda aka kama daya daga cikinsu ya labarta wa Aminiya cewa lokacin da ’yan bindigar suka fara harbi, ya ga wasu mutum uku a kan babur kirar CG DAYLONG na tsakiyarsu ke rike da bindiga yana harbi a lokacin da gungun matasa suka nufo wurin suna ihu. Ya ce daga nan sai suka tuka babur din suka nufi cikin gari suna harbin kan mai uwa da wabi.
Ya ce mutane na biye da su har suka fita babban titin hanyar Sakkwato a wurin mahadar titi kusa da gidan man Sule dan Farashi sai suka yi aron hannu inda suka ci karo da wani mai mota sai suka fadi. Ya ce mai motar ya fito don ya duba saboda a zatonsa ’yan acaba ne, fitowarsa ke da wuya sai mai bindigar ya bude masa wuta nan take ya mutu. “Abokansa da suke kan babur sai suka gudu shi kuma yana rike da bindiga yana harbi ya kasa gudu saboda bugun da motar ta yi musu ya karye a kafafunsa daga nan sai mutane suka yi ta jifansa har ya kasa yin komai sai muka kama shi muka mika wa ’yan sanda,” inji shi.
Wasu bayanai sun tabbatar wa wakilinmu cewa dan bindigar da aka kama ya ce su ba barayi ba ne, kuma an samu bindiga daya kirar AK 47 a hannunsa da kuma babur din da suka gudu suka bari.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kebbi, Mista Benjamin Onwuka ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yanzu haka daya daga cikin ’yan bidigar yana hannu kuma suna gudanar da bincike inda ya ce rundunar ba za ta iya tabbatar da ko barayi ne ba ko su wane ne har sai abin da bincike ya tabbatar.