’Yan bindiga sun halaka mutun 29 sun kona gidaje 40 a Kajuru
A ranar Talatar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga suka sake kai mummunan hari a kauyen Katmai da ke a Gundumar Maro a Karamar Hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna, inda suka bindige akalla mutum 29 kuma suka kona gidaje 40. Cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin akwai dan sanda daya da aka yi […]
Sufeto Janar Adamu Muhammad
A ranar Talatar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga suka sake kai mummunan hari a kauyen Katmai da ke a Gundumar Maro a Karamar Hukumar Kajuru da ke Jihar Kaduna, inda suka bindige akalla mutum 29 kuma suka kona gidaje 40.
Cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin akwai dan sanda daya da aka yi wa kwanton bauna a kan hanyarsu ta kai dauki ga al’ummar garin.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Abdurrahman ne ya tabbatar da aukuwar harin, ya ce tuni ya ziyarci kauyen domin jajanta wa wadanda aka hallaka musu ’yan uwa kuma aka lalata musu dukiya.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a yammancin ranar da abin ya faru. Ya ce, an kai harin ne a garin Katmai da safiyar ranar.
Kwamishinan ya ce maharan sun kona gidaje 40 tare da tarwatsa mazauna garin. Ya ce rundunar na iya bakin kokarinta wajen gano wadanda suka kai harin, inda ya ja hankalin mazauna yankin a kan daukar doka a hannunsu.
Ya ce hakkin hukuma ce ta kama wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukunci. “A yau (Talata) an kai hari a kauyen Karmai da misalin karfe 5:30 na Asuba a kusa da Gundumar Maro, wanda wadansu ’yan bindiga suka kai yankin. A lokacin da suka shiga garin suna ta harbin kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ashirin da tara, ciki har da wani dan sandanmu wanda suke kan hanyar kai dauki a garin,” inji shi.
Ya ce “Baya ga wannan kuma akwai akalla gidaje arba’in da maharan suka kona a yankin. Na ziyarci yankin tare da shugaban sojoji Birgadiya-Janar O.J Akpor da sauran jami’an ’yan sanda da na soji domin gane wa idanunmu abin da ya faru. Na kuma shawarci jama’a su kasance cikin zaman lafiya sannan mun jajanta wa ’yan uwan wadanda suka rasa rayukansu. Muna kuma ci gaba da yin bincike domin gano wadanda suka kai wannan hari domin hukunta su.”
Tun farko Kakakin Gwamnan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce gwamnati ta yi Allah wadai da wannan hari da aka sake kaiwa yankin. Ya kuma sha alwashin cewa gwamnati za ta tabbatar da an gano tare da kama wadanda suke da hannu wajen kai wannan hari a yankin.
Ya yi kira ga jama’a su yi hakuri su zauna lafiya, a yayin da jami’an tsaro ke kokarin bincike domin gano maharan.