’Yan bindiga sun hallaka miji, mata da ’yarsa suna tsaka da ibada

Wasu ’yan bindiga sun kai hari tare da hallaka wani magidanci, Ken Ekwesianya da matarsa da ’yarsa

’Yan bindiga sun hallaka miji, mata da ’yarsa suna tsaka da ibada

Masu Garkuwa da Mutane

Wasu ’yan bindiga sun kai hari tare da hallaka wani magidanci, Ken Ekwesianya da matarsa da ’yarsa a garin Azia na Karamar Hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Rahotanni sun ce an hallaka su ne ranar Alhamis da misalin karfe 7:00 na yamma a cikin wata coci.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani kan lamarin ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya ce tuni jami’an rundunar suka dukufa da bincike a kai.

Haruna ya ce, “Tuni muka fara bincike domin gano kisa nasu kuma nan ba da jimawa ba za mu kamo wadanda suka yi kisan domin su girbi abinda suka shuka.”