’Yan bindiga sun hallaka gomman mutane a Neja
Maharan sun bude wuta yayin da ake tsaka da cin kasuwa.
’Yan bindiga sun kashe mutanen da ba a san adadinsu ba a wani hari da suka kai wata kasuwa da ke unguwar Madaka a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.
Mazauna yankin sun ce maharan sun kai hari kasuwar ce da misalin karfe 3 na ranar Alhamis, lokacin da ake tsaka da cin kasuwa, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
- Dimokuradiyyar Najeriya na cikin hatsari — Bugaje
- Adadin mutanen duniya zai ragu nan da ƙarshen ƙarni — Bincike
Ya zuwa yanzu dai, babu wani cikakken rahoto game da harin.
Dtaya daga cikin mazauna yankin, ya ce mutane da dama da ba tantance adadinsu ba sun rasu a sakamakon harin.
Harin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wasu yan bindiga suka kai hari garin Pangu, inda suka kashe Hakimin gundumar da wasu mutum hudu.
Jin ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Birgediya Janar Mohammed Bello Abdullahi,ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ba.
Kazalika, shi ma kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, jin ta bakinsa ya ci tura.