‘Yan bindiga sun hallaka mutum 31 a Amurka

A kalla mutum 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin bindiga da aka kai a kan jama’a a garuruwan Dayton da ke Jihar Ohio da El Paso a Jihar Tedas wadda aka kai mata hari a wata cibiyar saye da sayarwa a garin El Paso duka a kasar Amurka. Jami’an tsaro sun ce an yi […]

‘Yan bindiga sun hallaka mutum 31 a Amurka

A kalla mutum 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin bindiga da aka kai a kan jama’a a garuruwan Dayton da ke Jihar Ohio da El Paso a Jihar Tedas wadda aka kai mata hari a wata cibiyar saye da sayarwa a garin El Paso duka a kasar Amurka.

Jami’an tsaro sun ce an yi nasarar kama wani matashi mai kimanin shekara 21 da ake zargi da kai harin El Paso wanda ya ci mutum 20.

Babban Jami’in ’Yan sanda yankin Greg Allen ya ce mutum 26 ne suka samu rauni a harin da aka kai a cibiyar kasuwancin ta Walmart da ke El Paso.

Allen ya  ce ana ganin  wanda ya kai harin yana da ra’ayin nuna kyama da wariyar launin fata.

Gwamnan Jihar Tedas, Greg Abbott ya ce a ranar da ya kamata a samu sukuni da walwala ne aka samu mutuwar jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba a wannan mummunan hari na ta’addanci a  Tedas.

Mafiya yawan mazauna yankin El Paso da ke kan iyaka da kasar Meziko suna magana ce da harshen Sifaniyanci.

An bayyana cewa harin na kan mai uwa da wabi shi ne irin sa na biyu mafi muni da aka kai kasar a cikin mako daya baya ga wanda aka yi a Jihar Kalifoniya.