’Yan bindiga sun hallaka mutum hudu a Ribas

’Yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun harbe mutum hudu a Kono Boue.

’Yan bindiga sun hallaka mutum hudu a Ribas

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun harbe mutum hudu a wani hari da suka kai yankin Kono Boue na Karamar Hukumar Khana ta Jihar Ribas.

Shaidu sun ce ’yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK 47, da ake zargi ’yan kungiyar asiri ne sun kutsa kauyen ne da tsakar dare ranar Asabar suna harbi a iska kafin daga baya su kashe mutum hudun.

Mai magana da yawun al’ummar, Golden Nwibakpo ya tabbatar da faruwar lamarin tare kokawa kan yawaitar kashe-kashe a Kono Boue.

Sai dai ya ce mutanen da aka kashe ba ’yan kungiyar asiri ba ne, mutanen kirki ne, shi ya sa lamarin ya haifar da fargaba har wasu mazauna na yin kaura daga yankin.

Nwibakpo ya bukaci Gwamnatin Jihar Ribas da Rundunar ’Yan Sanda Jihar su kafa ofishin ’yan sanda a yankin domin magance yawaitar ayyukan kungiyar asiri.

Kimanin mako biyu da suka gabata, ’yan bindiga sun kutsa Kono Boue suka kashe wani dattijo mai shekaru 58.

Wakilinmu ya nemi samun karin bayani daga Jami’in Hulda da Jama’a na Jihar Ribas, Nnamdi Omoni, amma bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka aike masa ba.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna