Mahara sun yi wa shugaban kasuwa kisan gilla

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu kisan gilla ne sun harbe  shugaban kasuwar Harbour dake jihar Delta

Mahara sun yi wa shugaban kasuwa kisan gilla

‘Yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu kisan gilla ne sun harbe  shugaban kasuwar Harbour dake karamar hukumar Udu ta jihar Delta, Misis Freedom Odiete har lahira.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, kuma wannan shine karo na uku da maharan ke neman rayuwarsa.

Mista Freedom dai wanda aka fi sani da Opito an yi masa kwanton bauna ne a yankin Ekete daidai mahadar babbar hanyar DSC a karamar hukumar.

Shaidun gani da ido sun ce marigayin na tsaka da tuki ne a motarsa kirar SUV jif lokacin da ‘yan bindigar suka yi masa dirar mikiya.

Daga nan ne suka harbe shi a kafadarsa ta dama inda ya yi karfin hali ya tsere amma suka sake bin shi har wurin da ya sami mafaka a kan hanyar Orhuwhorun suka ci gaba da harbinsa ba tare da kakkautawa ba.

Ko a makon da ya gabata dai sai da ya tsallake rijiya da baya sakamakon makamancin wannan harin.

Wasu majiyoyi dai sun ce harin ba zai rasa nasaba da wata cacar-bakin da ake yi tsakanin matasan yankin Ovwian da na Owhase kan mallakar wasu kasuwar.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta Delta, Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka suna nan suna farautar makasan ruwa a jallo.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu