’Yan bindiga sun harbe basarake a Kogi
Maharan sun nufi gidan basaraken kai-tsaye, inda suka hallaka shi har lahira.
Wasu ’yan bindiga sun kashe wani basaraken gargajiya (Onu), Mai Martaba Shagari Ebije’ego Job, a gidansa da ke Itama da ke Ƙaramar Hukumar Dekina a Jihar Kogi.
Maharan sun bi sawun Sarkin, wanda aka ce shi ne basaraken gargajiya mafi ƙarancin shekaru a ƙaramar hukumar, zuwa gidansa da yammacin ranar Litinin, inda suka harbe shi har lahira.
- Obasanjo bai halarci taron majalisar ƙasa da Tinubu ya kira ba
- Ambaliya: Mutum 3 sun rasu, dubbai sun rasa muhalli a Bauchi
Mazauna yankin, sun bayyana cewa ‘yan bindigar da har yanzu ba a tantance su waye ba, sun shiga garin, inda suka nufi gidan basaraken.
“Maharan da suka shiga garin da yawa an gansu ɗauke da makamai yayin da suka nufi hanyar gidan basaraken da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Litinin.
“Ba jimawa, sai muka fara jin ƙarar harbe-harbe daga yankin, lamarin da ya sa mutane suka riƙa tserewa domin neman mafaka.
“Wasu daga cikinmu sun fito ne bayan ‘yan bindigar sun fita daga garin suka gano cewa an kashe Mai Martaba Sarki a harin,” in ji wani mazaunin garin.
Ya ƙara da cewa garin ya shiga ruɗani domin da yawa sun fara yin ƙaura zuwa ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su.
Kakakin rundunar jihar, SP Williams Aya, bai amsa kira ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.