’Yan bindiga sun harbe dalibai bakwai a Damaturu
Wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ne sun kai hari a daren ranar Lahadi zuwa wata Sakandaren kwana ta Gwamnati GSS da ke cikin garin Damaturu a Jihar Yobe, inda suka halaka dalibai bakwai da malamai biyu a yayin […]
Wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ne sun kai hari a daren ranar Lahadi zuwa wata Sakandaren kwana ta Gwamnati GSS da ke cikin garin Damaturu a Jihar Yobe, inda suka halaka dalibai bakwai da malamai biyu a yayin da jami’an tsaro na JTF suka ce sun kashe biyu daga cikin ’yan bindigar.
Harin ya yi matukar girgiza al’ummar garin Damaturu ganin cewa an samu akalla kusan wata 10 ba tare da fuskantar wani hari ba a garin da a bara mazaunansa suka tarwatse saboda munanan hare-haren da ya fuskanta.
Wannan hari da ya auku da misalin karfe 9:11 na dare ya zo ne kasa da mako daya da gwamnatin jihar ta bada sanarwar kara lokacin walwala a garin daga karfe 9:00 na dare zuwa karfe 6.00 na safe sakamakon zaman lafiya da ya inganta a garin.
Wani dalibin makarantar da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa a daren ranar sun ga bakin fuskoki dauke da fitilu suna haskawa da zaga cikin makarantar da yawansu ya kai mutum 10, amma sai suka yi zaton sojoji ne ke sintiri. Ya ce can wani lokaci sai suka ji harbe-harbe a cikin makarantar kuma bayan kura ta lafa sai suka gano ’yan bindiga ne har sun kashe dalibai bakwai da malamansu biyu.
Kakakin Rundunar JTF Laftana Eli Lazarus ya tabbatar da faruwar hare- haren, ya ce jami’an rundunar sun kama uku daga cikinsu kuma sun wato makamai daga hannun ’yan bindigar da suka hada da bindigar AK 47 daya da sundukin da ke dauke da alburusai kimanin 258 da RPG da makamantansu.