’Yan bindiga sun harbe dan sanda

Ana zaman dar-dar bayan tsintar gawar dan sandan da ’yan bindiga suka kashe

’Yan bindiga sun harbe dan sanda

An tsinci gawar wani dan sanda da ’yan bindiga suka kashe a ranar Laraba a Owerri, Jihar Imo.

An tsinci gawar Sajan Loveday Obilonu ne a kwance an yi masa ruwan harsasai a cikin wani kwatami.

Wani dan kawunsa kuma dan jarida, Val Okara ya ce, “An harbe shi da harsashi akalla biyar a kansa. An harbe shi ne a cikin wata kwata, wanda ya sa ake zargin kisan kai ne. Ya kamata ’yan sanda su yi cikakken bincike.”

Mutuwar Sajan Loveday a kauyensu na Okwu-Uratta ya haifar da zullumi ganin yadda yankin Kudu maso Gabas ke fama da hare-haren haramtacciyar kungiyar IPOB a kan jami’an ’yan sanda da ofisoshinsu a baya-bayan nan.

Val, tare da taimakon jami’in ’yan sanda na shiyya mai kula da hedkwatar ’yan sanda na Orji, ne suka dauke gawar zuwa dakin ajiye gawa na Aladinma a Owerri.

Ya ce, “An gano wani harsashi da ba a yi amfani da shi ba a cikin magudanar ruwan da aka gawar a kwance. Akwai duk wani shakku cewa lamarin kisan kai ne. An gabatar da karar kisan a Hedikwatar ’yan sanda ta Shiyya ta daya.”

Amma kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo, Bala Elkana, ya ce ba a sanar da shi lamarin ba.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna