’Yan bindiga sun harbe dan sandan da ke tsaron Sarkin Bade
A makon jiya ne wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka bindige dan sandan da ke tsaron Mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Mai Umar Sulaiman da ake kira ADC Abubakar Sadik a kofar gidansa da ke Unguwar Sarkin Hausawa a garin Gashuwa da ke Jihar Yobe.Wata majiya ta […]

A makon jiya ne wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka bindige dan sandan da ke tsaron Mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Mai Umar Sulaiman da ake kira ADC Abubakar Sadik a kofar gidansa da ke Unguwar Sarkin Hausawa a garin Gashuwa da ke Jihar Yobe.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai hari ga ADC din ne da misalin karfe bakwai da rabi na yamma, bayan an idar da sallar Isha’i. Majiyar ta ce bayan da ’yan bindigar suka harbe Abubakar Sadik sai suka shiga harbe-harbe don razana al’ummar unguwar inda hakan ya sanya jama’a suka rika rugawa gidajensu don tsira da rayukansu.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Alhaji sunusi Ahmad Rufa’i ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har zuwa lokacin ba a kama kowa ba.
Wata majiya ta ce washegarin harin jami’an tsaro sun rika fatattakar mutanen garin suna dukansu, musamman mazauna unguwannin Zangon-Kanwa da Zangon-Takari da Sabon-Gari da ke garin Gashuwa. Wannan al’amarin ya jawo jama’a da dama sun samu raunuka ta dalilin dukan da suka sha a hannun jami’an tsaron da suka aiwatar da wannan samame.
Umar Aji Umar daya ne daga cikin wadanda wannan matsalar ta rutsa da shi ya shaida wa Aminiya ta waya cewa, “Muna zaune a majalisarmu mu bakwai da misalin karfe 11 na rana kawai sai muka ga motocin jami’an tsaro sun tsaya, bayan mun gaisa da su sai suka kira biyu daga cikinmu da suka je sai suka bukaci baki daya mu je. Muna isa suka ce mu kwakkwanta, sai kawai suka yi ta dukanmu, babu wanda ba su jiwa rauni ba kamar targade da fasa kai da kumbura hannu da sauran raunuka.”
Malam Umar ya ce wannan abin ya faru ne da rana tsaka, kuma ba wata dokar takaita zirga-zirga, kuma da suka zo ba su tuhume su da wani laifi ba.
Wani matashi da ya bukaci a sakaya sunanasa ya bayyana wa Aminiya ta waya cewa, “Muna nan zaune sai muka ga jami’an tsaro sun tsaya da motocinsu inda suka hau mu da duka, ni sun fasa min kai, wani daga cikin su ne ma ya zuba min ruwa na wanke jini sannan ya kawo min kyalle na daure kan.”
Kakakin Rundunar JTF mai aikin tabbatar da tsaro a Jihar Yobe Kyaftin Eli Lazarus ya shaida wa manema labarai cewa “Mun samu wannan labari amma muna gudanar da bincike kan yadda lamarin ya kasance.”