’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci

Matar Faston ta bayyana yadda maharan suka kai wa cocin hari cikin daren ranar Juma’a.

’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci

‘yan bindiga

’Yan bindiga sun kai hari wata coci da ke yankin Ogwashi-Uku a Jihar Delta, inda suka yi awon gaba da masu ibada a daren ranar Juma’a.

Sun harbi fasto sannan suka sace masu i ada shida a cocin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.

Sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na dare kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Delta.

Maharan sun harbi fasto, Apostle Divine Omodia, wanda yanzu haka yake kwance a asibiti.

Mutanen yankin suna cikin fargaba kan rashin tsaro a wuraren ibada, inda suke roƙon gwamnati ta ceto mutanen da aka sace tare da kama waɗanda suka kai harin.

Matar faston, Fasto Faith Omodia, ta bayyana jimaminta kan faruwar lamarin.

Ta ce ’yan bindigar sun buɗe wuta a cikin cocin.

“Na kwanta da jaririna a cikin coci sai na ji harbe-harbe. Kafin na ankara, harsasai sun fara shigowa cikin ɗakin da muke ciki.

“Ɗaya daga cikinsu ya harbe ni, amma harsashin bai shiga jikina ba. Sai dai kawai na ga wuta,” in ji ta.

Ta kuma ce an harbi mijinta a ƙafarsa, sannan ya rasa yatsu biyu.

Bayan haka, ’yan bindigar sun tattara masu ibada, tare da yin awon gaba da mutum shida, ciki har da masu gadin cocin biyu.

Mutanen da aka sace sun haɗa da Helen Onwuamaeze, Ariyo Emmanuel, Chike Okolo, da Blessing Waye, tare da masu gadi biyu da ba a bayyana sunayensu ba.

Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ba ta tabbatar da faruwar harin ba tukuna.

Lokacin da aka tambayi kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce babu wani rahoto da aka kai ofishin ’yan sanda kan harin.

Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP

Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno 

’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci