’Yan bindiga sun harbe hakimi har lahira a Filato

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da sanarwar kan harin ba.

’Yan bindiga sun harbe hakimi har lahira a Filato

’Yan bindiga sun kashe Hakimin Gwande da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos a Jihar Filato, Saf Samuel Alaket.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, yayin da hakimin ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan halartar taron Majalisar Sarakunan gargajiya a Bokkos.

Mazauna yankin sun ce maharan sun yi wa motarsa kwanton-ɓauna ne a kusa da iyakar gundumar Sha da al’ummar Daffo, kusa da garinsu.

Hakimin ya samu munanan raunuka a yayin harin, inda aka garzaya da shi wani asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Sai dai daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

Wani mazaunin yankin, Aten Pukat, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga al’ummar Gwande da ɗaukacin yankin Bokkos.

Shi ma shugaban matasan Bokkos, Christopher Luka, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa harin ya haifar da fargaba a yankin.

Sai dai ya ce shugabannin al’umma sun yi ƙoƙarin kwantar da hankalin jama’a, kuma yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.