’Yan bindiga sun harbe jami’an tsaro 12 a Kaduna

Hukumar tsaro ta Sibl Difens ce ’yan bindiga sun harbe jami’anta 7 da wasu ’yan bijilanti 5 har lahira a wurin hakar ma’adanai a Jihar Kaduna

’Yan bindiga sun harbe jami’an tsaro 12 a Kaduna

‘Yan Bindiga

Hukumar tsaro ta Sibl Difens (NSCDC) ta tabbatar da harbe jami’anta bakwai da wasu ’yan bijilanti biyar har lahira da ’yan bindiga suka yi a wurin hakar ma’adanai na Kuringa da ke Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Kakakin NSCDC, Olusola Odumosu ne ya bayyana hakan ga Aminiya ranar Talata a Abuja, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin da karfe 10:00 na safe.

Haka kuma ya ce jami’in hukumar guda daya ya tsira da munanan raunuka, kuma yana kwance a asibiti yana karbar magani gawarwakinsu kuma an ajiye su a mutuwaren Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.

Ya ce bayanai na nuna cewa sai da maharan suka kwashe makaman jami’an tsaron kafin su hallaka su.

An kama mutum uku da ƙwato wayoyin lantarki na sata 

Zan ci gaba da bada kuɗin hadaya kyauta — Gwamna Zulum 

Obasanjo na yunƙurin ɓata min suna don ɗan takararsa — Atiku

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane a Yobe