’Yan bindiga sun harbe likita da matarsa a Adamawa

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun harbe wani fitaccen likita mai suna Dokta Mwajim Malgwi a Yola babban birnin Jihar Adamawa tare da matsarsa. Dokta Malgwi, wanda shi ne ya mallaki Asibitin Polyclinic da ke Jimeta, rahotannni sun ce an kai masa […]

’Yan bindiga sun harbe likita da matarsa a Adamawa
’Yan bindiga sun harbe likita da matarsa a Adamawa

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun harbe wani fitaccen likita mai suna Dokta Mwajim Malgwi a Yola babban birnin Jihar Adamawa tare da matsarsa.

Dokta Malgwi, wanda shi ne ya mallaki Asibitin Polyclinic da ke Jimeta, rahotannni sun ce an kai masa hari ne yayin da yake hanyarsa da komawa gida daga gonarsa da ke kauyen Boggare kusa da Ngurore a Karamar Hukumar Yola ta Kudu, inda aka hallaka shi tare da matar tasa.

Wani makusancin mamacin, Ibrahim Walye, wanda ya ce ba zai iya kwatanta yadda lamarin ya faru ba, amma shaidu sun ce maharan sun biyo su ne da Keke-NAPEP, suka bude musu wuta suka tsere.

Kakakin ’Yan sandan Jihar, Othman Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce, yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike a yankin don gano maharan.

Likitan mai shekara 70, ya taba rike mukamin Kwamishinan Lafiya na Jihar Adamawa daga 1988 zuwa 1989.