’Yan bindiga sun harbe mai fafutikar kare hakkin bakar fata a Brazil

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana alhininsa da damuwa game da kisan nata.

’Yan bindiga sun harbe mai fafutikar kare hakkin bakar fata a Brazil

’Yan bindiga sun harbe wata shugabar al’ummar bakar fata a Arewa maso Gabashin Brazil da ta shahara wajen yaki da wariyar launin fata.

Wannan lamari dai ya jawo suka daga masu fafutuka da hukumomin gwamnati kamar yadda Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito.

Maria Bernadete Pacifico, shugabar kungiyar Quilombos a Brazil, wato kungiyar da bayi bakar fata suka kafa ta mutu bayan da wasu mutane biyu sanye da hular babur suka bindige ta, kusa da birnin Salvador na Jihar Bahia.

Matar wadda aka fi sani da Mama Bernadete, ’yar shekaru 72, ita ce babbar wakiliya a Majalisar Quilombos ta Brazil (CONAQ), kuma tsohuwar ministar daidaiton launin fata na birnin Simoes Filho da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Ta kuma yi fafutuka don ganin an yi adalci a kan kisan danta, Flavio Gabriel Pacifico dos Santos, wani shugaban al’umma wanda aka kashe shekaru shida da suka gabata.

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva wanda ya bayyana alhininsa da damuwa game da kisan nata, ya ce ma’aikatunsa na daidaiton launin fata da na kare hakkin bil’Adama sun aike da wakilai domin gudanar da bincike.

A nata bangaren ma’aikatar mata ta yi Allah wadai da kisan gillar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina

Zaɓen Edo: Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u

Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna