’Yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar UNIZIK, sun sace motarsa

Maharan sun tsere da motar malamin bayan harbe shi har lahira.

’Yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar UNIZIK, sun sace motarsa

’Yan Bindiga sun harbe malamin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK), Dokta Osita Chinedu, har lahira a daren Litinin a Jihar Anambra.

Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar sun tsayar da motar malamin, sannan suka harbe tare da tserewa da motarsa ƙirar Toyota Corolla launin toka.

Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta tabbatar da lamarin, tare da bayyana cewa ta fara bincike.

Sun buƙaci duk wanda ke da bayanan da za su taimaka wajen kama masu laifin ya kai rahoto zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa da shi.

Wannan harin ya tayar da hankali kan ƙaruwar rashin tsaro a jihar, musamman a cikin birnin Awka.

Mazauna yankin da abokan aikin marigayin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa don magance wannan matsalar tare da tabbatar da tsaron al’umma a jihar.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja