’Yan bindiga sun harbe manomi, sun sace matansa a Kaduna

Maharan sun harbe manomin ne yayin da yake dawowa daga gona da matansa biyu.

’Yan bindiga sun harbe manomi, sun sace matansa a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun harbe wani manomi tare da yin awon gaba da matansa biyu lokacin da suke dawowa daga gona a unguwar Maraban Jibo a ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin garin, Magaji Ibrahim, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6 na yamma.

Wani shugaban jama’a a yankin ya tabbatar da faruwa harin.

Ya ce ’yan bindigar sun kusa kashe mutumin amma sai suka gano cewa jini na fita daga ƙafarsa, sai suka ƙyale shi suka tafi da matansa.

Ya ce an tattara ’yan banga zuwa wajen da lamarin ya faru, inda suka kai manomin zuwa asibiti.

Ya ƙara da cewa har yanzu maharan ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka sace ba bare a yi maganar kuɗin fansa.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai ce uffan ba kan lamarin.

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza