’Yan bindiga sun harbe mutane 24 a Katsina
A kasuwar Jiƙamshi, ’yan bindiga sun harbe mutane bakwai yayin da ’yan kasuwa ke rufe shagunansu
Aƙalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da ’yan bindiga suka kai a ƙauyukan Jiƙamshi da Gwalgoro da ke cikin ƙananan hukumomin Musawa da Kankia a Jihar Katsina.
Harin na baya-bayan nan ya faru ne da yammacin Litinin a kasuwar Jiƙamshi, inda aka harbe mutane bakwai yayin da ’yan kasuwa ke rufe shagunansu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suka kashe ’yan ta’adda 45 a fafatawar da suka yi da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa.
Shaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 15 ɗauke da makamai a kan babura ne suka mamaye kasuwar, suka buɗe wuta sannan suka kwashe kaya na miliyoyin Naira.
- ’Yan sanda sun rufe shugabannin ACF a cikin Hedikwatar Ƙungiyar
- Jam’iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci na Kano
- Gwamnatin Tinubu tana zubar da ƙimar addinin Islama — Datti Baba-Ahmed
Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti (MACBAN) na Musawa ya tabbatar da cewa an riga an binne waɗanda suka mutu bisa tsarin Musulunci.
Ya bayyana harin a matsayin mummuna, yana mai kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai wani mai suna Malam Tukur Aliyu, wanda ya dawo daga Legas bayan bikin auren ’yarsa. Ya bar mata uku da ’ya’ya kusan 20 da sauran masu dogaro da shi.
Daya daga cikin matansa ta ce: “Rayuwarmu yanzu tana cikin haɗari. Shi ne ginshiƙinmu, yanzu ya tafi, ba mu san yadda za mu rayu ba.”
Haka nan, Rabi’u Ashiru, mai shekaru 35, wanda ke sana’ar sayar da wayoyi da katin waya, ya rasa rayuwarsa a shagonsa, a yayin da ake shirin aurensa cikin ’yan watanni masu zuwa.
Mahaifinsa, Ashiru Ba Zama, ya ce: “Mun rasa ginshiƙin iyali. Shi ne ke biyan kuɗin makaranta da ciyar da mu. Yanzu mun shiga wani hali.”
Wani tsohon mamba na kwamitin tsaro na Jiƙamshi, Bilyaminu Abubakar, ya bayyana hare-haren a matsayin shiri na lalata yankin.
Ya ce: “Waɗanda suka ce sun tuba amma ba su ajiye makamai ba, har yanzu suna addabar al’ummarmu. Hukuma ta sani amma ba a ɗaukar mataki mai ƙarfi.”
Wani magidanci da aka kashe a harin, Umar Salisu, mai shekaru 55, ya bar mata biyu da ’ya’ya kusan 16. Matarsa, Amina, ta ce: “Mun kaɗe. Ba mu san makomar iyalinmu ba.”
Abokin marigayin, Nura Jiƙamshi, ya yi kira ga gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa don kauce wa rikicin jin ƙai. Ya ce: “Ina rokon a tallafa wa iyalan waɗanda suka mutu.”