‘Yan bindiga sun harbe mutum shida a Benuwe
Wannan lamari ne na ramuwar gayya a cewar wani ɗan Majalisar Dokokin Binuwai.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum shida a wani hari da suka kai wasu wurare uku ciki har da wata kasuwa a Ƙaramar hukyumar Katsina-Ala ta Jihar Benuwe.
Ganau sun shaida wa wakilinmu a birnin Makurdi cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun far wa wuraren ne a kan babura.
Daya daga cikin shaidun da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce ‘yan bindigar sun ƙaddamar da hare-haren ne a yankin Tor Donga da ke Unguwar Utange, da unguwar Gugu a gundumar Michihi da kuma wani wuri a gundumar Mbacher.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina-Ala ta Gabas a Majalisar Dokokin Binuwai, Jonathan Agbidye, ya bayyana takaici da kan faruwar lamarin da ya bayyana a matsayin ramuwar gayya.
Dan majalisar ya ce, “Waɗancan mutanen da ke wannan unguwar sun taɓa samun saɓani da maharan.
“Sun yi sa”a sun kama biyu daga cikinsu a cikin Afrilu kuma suka kashe su. Don haka wannan manufa ce kawai ta ramuwar gayya.
“Amma a yanzu an samu kwanciyar hankali. Mun je unguwar tare da ‘yan sanda da safiyar Laraba.”
Da aka tuntuɓi jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene ta ce ba ta da masaniya kan lamarin.