‘Yan bindiga sun harbe ‘Yan Sanda 3 a Sanga
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wasu jami’an ‘yan sanda uku da ke aiki a shingen duba ababen hawa da ke tsakanin Fadan Karshi zuwa Saboke Karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna. Wani ganau daga yankin ya shaidawa Aminiya cewa, maharan da ke kan abin hawa sun […]
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wasu jami’an ‘yan sanda uku da ke aiki a shingen duba ababen hawa da ke tsakanin Fadan Karshi zuwa Saboke Karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.
Wani ganau daga yankin ya shaidawa Aminiya cewa, maharan da ke kan abin hawa sun bude wuta ne nan take da isowarsu wajen inda direban motar ‘yan sandan ya sha da kyar bayan ya tsere zuwa cikin daji.
Wannan lamarin yana zuwa ne jim kadan bayan kaddamar da Karamin barikin sojoji a garin Gwantu, hedkwatar Karamar hukumar ta Sanga don bunqasa harkokin tsaro a yankin.